An saki fursunonin siyasa 52 a Belarus

[ad_1]



Gwamnatin Belarus ƙarƙashin jagorancin Shugaba Alexander Lukashenko ta saki fursunoni siyasa 52 ciki har da fitaccen ɗan adawa, Mikola Statkevich da kuma ɗan jarida Ihar Losik, a wani yunƙuri da aka danganta da ruwa da tsakin Amurka.

Shugaban Lithuania, Gitanas Nauseda, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X (Twitter), yana mai cewa: “Mutum 52 da aka daure bisa dalilan siyasa sun tsallako kan iyaka daga Belarus zuwa Lithuania lafiya.”

Ya ce yana “matuƙar godiya” ga gwamnatin Amurka da Shugaba Donald Trump bisa rawar da suka taka wajen sasantawa da cimma wannan matsaya.

Daya daga cikin wadanda aka sako shi ne Mikola Statkevich, ɗan adawa mai shekaru 69 da haihuwa, wanda ya tsaya takarar shugabancin ƙasar a shekarar 2010, inda ya shafe shekaru biyar a gidan yari.

Haka zalika, Ihar Losik, ɗan jarida mai shekaru 33 daga Radio Free Europe/Radio Liberty, shi ma ya shafe shekaru biyar a tsare kafin a sako shi.

Hukumar dillancin labarai ta Belarus, Belta, ta ruwaito, cikin wadanda aka sako akwai ’yan ƙasashe 14 na waje, da suka hada da ’yan Lithuania 6, ’yan ƙasashen Latvia, Poland da Jamus biyu-biyu, sai kuma ’yan ƙasashen Faransa da Birtaniya daya-daya.

Mafi shahara cikin ’yan ƙasashen wajen da aka saki ita ce Elena Ramanauskiene, wata ’yar kasar Lithuania da aka daure a bara bisa zargin leken asiri.

Sai dai har yanzu akwai fursunoni sama da 1,000 da ke tsare kamar yadda Shugaba Nauseda ya bayyana yana mai kiran da a saki sauran fursunonin siyasa.

“Har yanzu fiye da mutum 1,000 na tsare a gidajen yari na Belarus. Dole ne mu ci gaba da ƙoƙari har sai an ba su ’yanci!”

A watan Yunin da ya gabata, Belarus ta saki wasu fursunoni siyasa 14, ciki har da Sergei Tikhanovsky, mijin Svetlana Tikhanovskaya, shugabar ’yan adawa da ke gudun hijira.

A shekarar 2020, dubban ’yan ƙasar Belarus suka gudanar da zanga-zangar ƙin amincewa da sakamakon zaɓe, wanda Lukashenko ya lashe karo na shida, lamarin da ya janyo matakin murƙushe ’yan adawa, waɗanda da dama-dama aka ɗaure su, kamar yadda ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam suka bayyana.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *