Trump ya yi barazanar lalata cibiyar iskar gas ta Iran

[ad_1]



Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar lalata wata babbar cibiyar samar da iskar gas ta Iran, sai dai idan ta daina kai hare-hare kan wuraren samar da makamashi na ƙasar Qatar, waɗanda suka fuskanci gagarumar asara a ranar Alhamis.

Farashin ɗanyen mai ya yi tashin gwauron zabi da kashi biyar cikin 100 sakamakon fargabar yaƙin Gabas Ta Tsakiya da aka kwashe kusan makonni uku ana yi zai iya yin lahani na din-din-din ga hanyoyin samar da makamashi na duniya.

Iran ta ƙaddamar da jerin hare-hare kan wuraren makamashi na yankin Tekun Fasha, ciki har da babbar cibiyar iskar gas ta Ras Laffan da ke Qatar, a matsayin martani ga harin da Isra’ila ta kai wa cibiyar samar da iskar  ta “South Pars” da ke Iran — wadda take matsayin babban wurin adana iskar gas mafi girma a duniya.

Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta inda ya buƙaci a daina kai hare-hare kan wuraren makamashin Iran da na Qatar baki ɗaya.

Ya bayyana cewa, Amurka “ba ta san komai ba” game da harin da Isra’ila ta kai wa South Pars a baya, inda ya yi alƙawarin cewa, “ISRA’ILA BA ZA TA SAKE KAI WANI HARIN BA” kan wannan wurin muddin Iran ta daina kai hari Qatar.

To sai dai, Trump ya yi gargaɗin cewa, idan har Iran ba ta bi wannan umarnin ba, Amurka za ta “lalata baki ɗayan cibiyar samar da iskar gas ta South Pars baki ɗayanta.”

‘Gagarumar Asara’

Farashin makamashi ya riga ya tashi tun bayan da jigilar jiragen dakon mai ta mashigar ruwa ta “Strait of Hormuz” — wadda yawanci ke ɗaukar kashi ɗaya bisa biyar na man fetur ɗin duniya — ta kusan tsayawa cik saboda barazanar hare-haren Iran.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *