Harin Iran a Saudiyya ya jikkata sojojin Amurka 12

[ad_1]



Sojojin Amurka 12 sun jikkata a harin da Iran kai kan sansanin soji na Yarima Sultan da ke Saudiyya.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters sun bayyana cewa, sojojin Amurka 12 sun jikkata a harin da Iran ta ka Sansanin Sojin Sama na Yarima Sultan da ke Saudiyya.

Jami’an Amurka sun tabbatar da cewa biyu daga cikinsu sun samu munanan raunuka.

Wannan ya ƙara yawan sojojin Amurka da suka jikkata zuwa sama da 300, tun bayan ɓarkewar yaƙin da aka fara da Iran a ranar 28 ga Fabrairu.

Rundunar Amurka ta ce a ranar Juma’a, daga cikin su, 273 sun riga sun koma bakin aiki.

A halin yanzu, sojojin Amurka 13 ne suka rasa rayukansu tun bayan fara wannan rikici.

A gefe guda kuma, Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) na shirin ƙaddamar da hare-haren ƙasa a Iran cikin makonni masu zuwa.

Jaridar Washington Post ta ruwaito a ranar Asabar cewa, shirin na iya haɗawa da kai samame daga sojojin ƙasa.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar ba ko Shugaba Donald Trump zai amince da waɗannan shirye-shirye.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *