Ba za a yi sulhu da Iran ba sai dai ta miƙa wuya ba tare da sharaɗi ba — Trump
[ad_1]
Shugaban Amurka Donald Trump ya buƙaci Iran ta miƙa wuya ba tare da wani sharaɗi ba, yana mai cewa hakan ne kaɗai hanyar da za a kawo ƙarshen yaƙin da ake yi.
Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, inda ya ce bayan Iran ta miƙa wuya za a zaɓi sabbin shugabanni da za su samu karɓuwa, sannan Amurka da ƙawayenta su taimaka wajen sake gina tattalin arziƙin ƙasar.
Ya ce: “Ba za a yi sulhu da Iran ba, sai dai ta miƙa wuya ba tare da wani sharaɗi ba. Bayan haka za a zaɓi shugabanni masu kima da karɓuwa, sannan tare da abokan hulɗa za mu yi aiki don sake gina Iran domin ta zama mai ƙarfi a fannin tattalin arziƙi fiye da kowane lokaci.”
Sai dai Trump bai fayyace a sarari abin da yake nufi da wannan tsari ba.
Furucin na Trump ya zo ne duk da cewa gwamnatin Amurka ta bayyana cewa manufar haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila a yaƙin da ake yi ba wai kifar da gwamnatin Iran ba ce.
Sai dai wasu kalaman Trump na baya-bayan nan sun nuna yana son taka rawa wajen zaɓen sabon shugabanci a Iran bayan mutuwar jagoran addinin ƙasar, Ali Khamenei, wanda aka kashe a wani hari a farkon yaƙin.
A kawo ƙarshen yaƙin —MDD
A gefe guda kuma, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi kira da a kawo ƙarshen faɗan.
Guterres ya ce tashin hankalin da ake samu a yankin Gabas ta Tsakiya na haddasa mummunar illa ga fararen hula, yana mai jaddada buƙatar komawa teburin sulhu domin dakatar da yaƙin.
Ba mu ƙayyade lokacin kawo ƙarshen yaƙin ba — Trump
Game da tsawon lokacin da yaƙin zai ɗauka, Trump bai bayar da cikakken bayani ba.
Sai dai a wasu lokuta a bayan nan ya ce rikicin na iya ɗaukar makonni huɗu zuwa biyar, amma ya jaddada cewa Amurka za ta ci gaba da fafatawa muddin ya zama dole, ko da kuwa yaƙin ya ɗauki lokaci mai tsawo.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link