Juyin mulki: Shugaba Rajeolina ya tsere daga ya rushe majalisa

[ad_1]



Shugaban Madagascar, Andry Rajoelina, ya tsere daga ƙasar a yayin da rikicin soja da ke neman kifar da gwamnatinsa ke ƙara ƙamari.

A ranar Talata ya sanar da rushe majalisar Dokoki ta Ƙasar, a daidai lokacin da ake fama da tarzomar soja da ta tilasta masa tserewa daga ƙasar.

A cewar wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta wallafa a shafinta na Facebook, Rajoelina ya fitar da wata doka da ke umartar rushe majalisar dokoki nan take.

Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da wasu dakarun soja na musamman suka goyi bayan zanga-zangar matasa da ke neman sauya gwamnati, lamarin da ya haifar da ƙoƙarin juyin mulki.

Shugaban ya bayyana a wani jawabi da aka yaɗa ta kafafen sada zumunta a daren Litinin cewa ya fice daga ƙasar ne saboda tsoron rasa rayuwarsa.

Majalisar dokoki dai ta kasance cikin wani zama na musamman don tattauna yiwuwar tsige Rajoelina daga shugabancin ƙasa, amma rushewar da ya yi wa majalisar ya daƙile wannan yunƙuri gaba ɗaya.

Wannan doka da Rajoelina mai shekaru 51 ya fitar ta ƙara dagula siyasar Madagascar, mai yawan jama’a kimanin miliyan 31 a gabar tekun gabashin Afirka.

Tun wasu makonni da suka gabata, Rajoelina na fuskantar matsin lamba daga gungun matasa ’yan Gen Z da ke jagorantar zanga-zangar neman sauya gwamnati.

Aminiya ta fahimta cewa har yanzu ba a san inda shugaban ke ba, yayin da halin rashin tabbas ke ci gaba da mamaye al’amuran siyasa a ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *