Amurka ta ƙwace jirgin dakon mai na Rasha a Tekun Atlantika

[ad_1]



Gwamnatin Amurka ta sanar da ƙwace wani jirgin dakon mai da ake alaƙanta shi da Rasha a Tekun Atlantika, bayan bin diddiginsa tun daga gabar tekun Venezuela.

Amurka ta ce jirgin na daga cikin jiragen ruwan da aka basaja da su wajen yi wa Venezuela, Rasha da Iran safarar mai, abin da ta ce ya saɓa wa takunkuman da ta ƙaƙaba.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa an ƙwace jirgin ne duk da cewa sojojin ruwan Rasha na yi masa rakiya.

A cewar rundunar sojin Amurka a Turai, an ɗauki matakin ne bisa umarnin wata Kotun Tarayya ta Amurka a yayin da Gwamnatin Trump ta ce takunkumin hana fitar da man Venezuela zai yi aiki “a ko’ina a duniya”.

Sai dai Rasha ta soki matakin, tana mai cewa dokar ’yancin zirga-zirgar ruwa a manyan tekuna ta ba da damar irin wannan tafiya, tare da buƙatar a saki fasinjojin da ke yi wa jirgin rakiya.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin, wanda aka fi sani da Bella-1, ya sauya suna zuwa Marinera tare da rajista ta Rasha, har ma aka zana tutar Rasha a jikinsa, lamarin da Amurkan ta ce jirgin ba shi da halastacciyar ƙasa.

Sojojin Amurka sun kuma sanar da ƙwace wani jirgin mai na biyu a Tekun Caribbean, wanda ya kai adadin jiragen da ta ƙwace tun watan da ya gabata zuwa huɗu.

Matakin ya zo ne bayan Amurka ta kama Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, inda Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta riƙa sarrafawa da sayar da man Venezuela, sannan kuma kuɗin za a ajiye su ne a asusun da Amurka ke iko da shi.

Masu sharhi na ganin wannan lamari na ƙara nuna tsauraran matakan da gwamnatin Trump ke ɗauka kan Venezuela da kuma siyasar mai a duniya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *