Trump ya tsawaita wa’adin dakatar da kai wa Iran hari
[ad_1]
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da ƙara jinkirta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Iran na tsawon kwanaki 10, domin tattaunawar sulhu ta ci gaba da gudana.
Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, inda ya ce matakin ya biyo bayan abin da ya kira “ci gaba mai kyau” a tattaunawar da ake yi da Iran, duk da cewa Tehran ta musanta cewa akwai wata tattaunawa kai tsaye.
Rahotanni sun nuna cewa za a ci gaba da jinkirta harin har zuwa ranar 6 ga watan Afrilu, a wani mataki na ƙoƙarin rage zafin rikicin da ya shafe kwanaki 27 ana gwabzawa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Duk da wannan yunƙuri, hare-hare na ci gaba da aukuwa a yankin, musamman a ƙasashen Gulf, baya ga Iran da Isra’ila, lamarin da ke ƙara tsananta fargabar yaƙi mai faɗi.
Wani babban jami’in sojin Iran da bai bayyana sunansa ba ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Tehran ta karɓi saƙon tayin Amurka, amma ta zargi saƙon da nuna son kai da ɓangaranci.
A ɓangaren asarar rayuka kuwa, mataimakin ministan lafiya na Iran, Ali Jafarian, ya ce hare-haren ƙawancen Amurka da Isra’ila sun kashe mutane 1,937 a cikin ƙasar.
Haka kuma, Ministan Harkokin Wajen Pakistan, Ishaq Dar, ya tabbatar da cewa ƙasarsa na taka rawa wajen isar da saƙonni tsakanin Amurka da Iran a wani yunƙuri na shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin.
Ya ce yaƙin ya riga ya yi sanadin mutuwar sama da mutane dubu uku cikin ƙasa da wata guda.
Sai dai duk da jinkirta harin, Trump ya ci gaba da gargaɗin cewa Iran za ta fuskanci sakamako mai tsauri idan ta ƙi amincewa da buƙatun Amurka.
A gefe guda kuma, rahotanni sun nuna cewa Amurka na ci gaba da tura ƙarin sojoji zuwa yankin, lamarin da ke nuna cewa duk da tattaunawar, ana ci gaba da shirin ko-ta-kwana.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link