Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin (2)
[ad_1]
…cigaba daga makon da ya gabata.
Alkur’ani Babbar Ka’ida Ce Ta Ilimi
Shehu Ismaila Umar Almadda ya bayyana cewa, Manzon Allah SAW ya nuna adalci a tsarin halitta, ya kuma cika kyawawan dabi’un annabawa.
Ya karantar da Larabawa da duniya ilimi, ta hanyar tsame su daga duhun jahilci zuwa hasken Ilimi.
Alkur’ani, babbar ka’ida ce ta ilimi, duk wani tsarin Ilimi da ka’idarsa, Alkur’ani ya tattare komai. Da wannan za mu kara tabbatar da cewa, lallai Annabi SAW ba kusa yake da sauran Annabawa ba, ya zarce su nesa a komai.
Ubangiji tabaraka wata’ala ya bai wa Annabi Musa AS, ayoyi 9 na mu’ujiza, amma Annabi SAW, komai nasa aya ce, wanda Alhamdulillah, a wannan zamani, an fara ganin ayoyin Alkur’ani da ido, kuma kafin duniya ta kare sai komai ya fito fili.
Komai dake cikin Alkur’ani, a bayyane yake, babu cakudi. Ubangiji ya halicci halittar sammai da kassai kuma an ganta ta fita lafiya kalau, ta kaka, wanda ya yi halitta bai cakuda ta ba amma kuma zai cakuda bayaninta? Lallai, Ubangiji bai cakuda bayanin aikin sa ba. Duk wanda ya ga cakudi a Alkur’ani, to shi ne ya cakuda – rashin fahimtarsa ce kawai.
Domin samun ingantaccen ilimi, duk kira’ar Kur’ani da aka ce shazza ce (a daina aiki da ita), ya dace a nemo ta, mafi yawanci siyasar wannan zamani ce ta sanya aka ce shazza ce, kamar kira’ar Sayyadina Ali, da Abdullahi bin mas’ud, da sauransu sabida ba su bai wa gwamnati kira’o’insu ba a kona, duk da cewa, Ubangiji ya fadawa Annabinsa a Alkur’ani cewa: “kulma yakunuli an ubaddilahu min tilka’i nafsi – bai dace a gare ni ba, in sauya abin da aka saukar min a kashin kaina”, don haka, mu dai ga karatu nan amma kar a yi gaggawar fassara shi, lokacin shi zai yi, “la tuharrik bihi lisanaka lita’ajala bihi, inna alaina jam’ahu wa kur’anahu – kar da ka yi gaggawar fassara shi, aikinmu ne tattara shi da kuma bayanin shi).
Asalin Ilimin komai kur’ani ne, musamman lissafi, “wa ahsa kulla shai’in ilma; wa ahsa kulla shai’in adada.” Da gwaje-gwaje ake samun natijar ilimi, kuma da sauye-sauye ne za a kai ga kiyama.
Bai Kamata Al’umma Su Rika Takure Shari’ar Addinin Annabi SAW Ba
A ci gaba da karatun Tafsirin Alkur’ani Shehu Ismaila Umar Almadda (Mai Diwani) ya yi bayani cewa, tsarin (Millah), wanda ubangiji yace, Annabi SAW ya tsaya akan shi, tsari ne na Annabi Ibrahim (AS) wanda ya kunshi rahama da tausayi a cikin dukkanin hukunce-hukunce, shi yasa kullum take canzawa da canzawar zamani (hanifiyya).
Shehun Malamin, yace duk yanda bangarorin ilmi suka gurbata hukunci na addinin Annabi SAW, to asalin hukuncin da ka’idodin shari’arsa yana nan lafiya kalau babu abin da zai same shi saboda ba “haddu” bace, “huduudu” ce, ma’ana akwai ‘yanci na zabi, misali, hukuncin kisa zai iya saukakuwa zuwa diyya ko daurin rai-da-rai.
Shehu Almadda yace, duk Musulmi yana kan tsari ne na Annabi Muhammad SAW, Amma bai kamata al’umma su rika takure shari’ar addinin Annabi Muhammad da siyasa ta bangaranci kamar yadda yake faruwa a wasu sassan duniya a yanzu. Tsarin Manzon Allah SAW, tsari ne na Allah wanda ya tsara masa kuma shi ne daidai.
Shehun Malamin ya kara da cewa, duniya taga Dauloli da yawa wadanda aka kafa amma duk daga karshe sun rushe, amma ita daular Manzon Allah SAW, hanifiyya ce (mai canzawa da canzawar zamani), ita tana nan daram har karshen zamani, ba zata fadi ba domin ita ce daular Allah. Kuma ba kowane tsari na zamani ne za a ce ya saba ma tsarin Allah ba, sai dai in an ga tsarin ya yi karo da Alkur’ani ko hadisan Manzon Allah SAW. Wannan yasa ba kowace fatawa ce abin hukunci ba har sai an auna ta da mizanin Shari’a (Alkur’ani da Hadisi). Don haka, ya kamata al’umma su kula da masu fatawa, su auna fatawoyin da suka yi kafin su yi amfani da su.
Addinin Annabi SAW, Ya Dace Da Kowane Zamani
Mai Diwani ya cigaba da bayyana hikimomi da sharhi wanda Suratu Namli ta tattaro. Karatun yana gudana ne cikin tsari, zurfin ilimi da kuma fahimtar zamani.
Addinin Annabi (SAW), addini ne Hanafiyyi, wanda yake samun ci gaba kuma ya kasance mai sassauci da dacewa da kowanne zamani. Ya jaddada cewa duk inda ilimi da binciken zamani suka kai, za a same su a cikin koyarwar addinin Musulunci.
Malamin ya yi nuni da yadda Turawa suka sauya tunani daga tsarin jagorancin malaman addini zuwa tsarin shugabanci mai kula da ilimin kimiyya da bincike tun kusan shekaru 1400 na Miladiyya, abin da ya taimaka musu wajen samun ci gaba. Ya ce wannan sauyi ya zama darasi ga al’umma, inda ya ambaci yadda aka taba tura malamai daga Kano zuwa kasashen waje domin su ga irin wayewar da ake samu, su kuma kawo ta gida, duk da cewa wannan “Failar” (wayewar zamani) a gare mu, har yanzu ba ta kai shekaru 100 ba.
Haka nan, ya soki ra’ayoyin da ke jingina durkushewar al’umma ga tufafi ko al’adu kadai, yana mai cewa matsalar ta fi zurfi a bangaren da ya shafi ilimi, tsari da kuma aiki tukuru. Ya yi karin haske kan asalin harshe da tarihi, tare da bayyana bambance-bambancen Larabci (na Yemen, Misira da wasu yankuna), tare da jaddada cewa Alkur’ani “Arabiyun Mubin” ne watau da harshen Larabci ake fahimta cikin sauki.
A bangaren littattafan da suka gabata kuwa, ya bayyana cewa Attaura ta shafi al’umma da kabila a kebance (kamar Annabi Musa da mutanensa), yayin da Alkur’ani kuwa ya zo ne ga dukkan bil’adama kuma ya dace da kowanne zamani. Ya ambaci tarihin wasu al’ummomi a Yemen da suka riga Musulunci shekaru dubbai, da kuma ruwayoyi da fatawowi daga manyan malamai kamar Imam Malik. Haka nan ya ambaci ra’ayin Ka’abu bin Malik game da sauye-sauyen da suka shafi addini, yana mai jaddada cewa Alkur’ani ne kadai zai mayar da al’umma kan abubuwa yadda suka kamata.
Shehu Mai Diwani, ya yi bayani kan ka’idar kauna a cikin Alkur’ani tare da koyarwar Annabi (SAW) kan kauce wa cutarwa, da guje wa yawaita maganganu, da kuma gina kyawawan dabi’u. Ya jaddada cewa fitirar Allah ita ce imani da Allah, aikata alheri, nisantar shirka, da bin tsari da doka domin rayuwa mai tsawo da amfani a duniya da lahira.
A karshe, malamin ya yi bayani kan Wasikar Madina (tsarin zamantakewa) da Annabi (SAW) ya kafa, wadda ta kawo tsari, zaman lafiya da hakin kan kabilu daban-daban a gari daya, tare da kira ga sakar wa al’umma mara ta yi nishadi a cikin addini domin gujewa tsanani da taurin zuciya.
Duk Kasa Ko Al’umma Da Ta Kafa Tsari Bisa Adalci, Tausayi, Ilimi, Da ‘Yanci Za Ta Samu Zaman Lafiya Da Dorewa
Shehu Ismaila Umar Almadda (Mai Diwani) ya jaddada cewa addinin Musulunci addini ne na sauki, hikima da tausayin halitta—ba na tsanani ko tilas ba.
Ya kara jaddada cewa, duk wata daular Musulunci ba za ta ji tsoron juyin zamani ba muddin tana tafiya bisa hukuncin Alkur’ani, da fahimtar zamani.
A yayin tafsirin, Mai Diwani ya tunatar da yadda Annabi (SAW) ya gina al’umma bisa tausayi da ilimi, ba tare da tilasta addini ba: “La ikraha fid-din”. Addinin Musulunci ya bai wa mutane ‘yancin ibada, siyasa da kasuwanci cikin adalci, tare da kiyaye hakkin kowa. An nuna cewa sauye-sauyen zamani ba laifi ba ne idan suna gina mutum da al’umma.
A bangaren al’ada da sutura, an fayyace cewa Musulunci bai takaita mutane da irin kaya daya ba—abinda ake nema shi ne rufe tsiraici da mutunci. Rawani ba shi ke nuna Malanta ba, daya ne daga cikin al’adun Larabawa.
Shehin Malamin, ya yi gargadin cewa, duk kasa ko al’umma da ta kafa tsari bisa adalci, tausayi, ilimi da ‘yanci, za ta samu zaman lafiya da dorewa; amma duk wadda ta rungumi zalunci da karya, sakamakonta rushewa ne.
[ad_2]
Source link