Saraki Ya Soki Gwamnatin Kwara Kan Ƙaruwar Rashin Tsaro
[ad_1]
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya soki yadda ake tafiyar da tsaro a Kwara. Ya ce gwamnatin jihar ba ta ɗauki matakan da suka dace wajen daƙile matsalar ba.
Saraki ya bayyana hakan a wata hira, inda ya kwatanta halin yanzu da lokacin da yake gwamna. Ya ce daga 2003 zuwa 2019, jihar ba ta fuskanci irin wannan matsala ba.
- Jam’iyyar PDP Za Ta Dawo Da Karfin Ta Bayan Babban Taron Kasa – Saraki
- Majalisar Tarayya Na Ƙoƙarin Zama Ƴar Amshin Shata – Saraki
Ya jaddada cewa bayanai na nuna taɓarɓarewar tsaro a fili. Ya ce bai kamata a siyasantar da batun tsaro ba, domin gaskiya a bayyane ta ke.
Saraki ya buƙaci a fi mai da hankali kan rigakafin laifuka maimakon jiran faruwarsu. Ya ce a zamaninsa ana yin tarukan tsaro akai-akai tare da jami’an tsaro.
Ya kuma bayyana cewa ‘yan bindiga na komawa wuraren da ba a tsaurara matakan tsaro ba. Ya ce hakan ya sa suka fara kai hare-hare a yankunan da ba su saba ba.
Ya zargi gwamnati da gazawa wajen tinkarar barazanar da ke tasowa. Ya ce maimakon gyara kura-kurai, ana danganta suka da siyasa.
[ad_2]
Source link