Alassane Ouattara ya lashe zaɓen Ivory Coast karo na huɗu
[ad_1]
Shugaba Alassane Ouattara, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙasar Ivory Coast wanda ya ba shi sabon wa’adin mulki a karo na huɗu.
Ouattara mai shekaru 83, ya samu kashi 89.77 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa ta tabbatar a ranar Litinin.
Fiye da mutane miliyan tara ne suka cancanci kada ƙuri’a a zaben da aka gudanar a ranar Asabar, wanda aka gudanar cikin yanayi na fargaba, bayan da manyan abokan hamayyarsa biyu — tsohon shugaban ƙasa Laurent Gbagbo da tsohon shugaban Credit Suisse, Tidjane Thiam — aka hana su tsayawa takara.
Sakamakon ya nuna cewa, duk da ƙarancin fitowar masu jefa ƙuri’a a wasu sassan ƙasar, Ouattara ya samu rinjaye har ma a yankunan da ake ganin masu adawa ke da tasiri.
Tsohon Ministan Kasuwanci, Jean-Louis Billon ne ya zo na biyu da kashi 3.09 cikin 100, sai kuma matar tsohon shugaban ƙasa, Simone Gbagbo ta samu kaso 2.42, yayin da hukumar zaɓe ta bayyana cewa adadin waɗanda suka kaɗa ƙuri’a sun kai kashi 50.10 cikin 100 — kwatankwacin na shekarar 2020.
Masana harkokin siyasa sun ce rashin halartar manyan ‘yan adawa da kiran su na a ƙaurace wa zaɓen ya sa jama’a da dama suka ƙi ita kaɗa ƙuri’a.
Sai dai duk da nasarar da Ouattara ya samu, jam’iyyun adawa sun ƙi amincewa da sakamakon, inda suka buƙaci a gudanar da sabon zaɓe.
Rahotanni sun ce aƙalla mutane takwas ne suka mutu yayin tarzomar da ta barke kafin zaben, lamarin da ya sa gwamnati ta kafa takunkumin fita da dare a wasu yankuna tare da jibge jami’an tsaro 44,000 don tabbatar da tsaro.
A yanzu haka dai harkokin yau da kullum kamar yadda aka saba sun kankama a birnin Abidjan bayan sanar da sakamakon zaɓen da wasu jaridu ke yabawa a matsayin “zaɓe na kwanciyar hankali,” yayin da wasu ke cewa ya sake nuna rarrabuwar kawuna a ƙasar.
Ouattara ya fara hawa mulkin Ivory Coast ne bayan rikicin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2010-2011 tsakaninsa da Laurent Gbagbo, wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 3,000 daga ɓangarorin magoya bayansu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link