Trump ya ƙaddamar da kwamitin tabbatar da zaman lafiya a duniya
[ad_1]
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ƙaddamar da wani sabon kwamitin tabbatar da zaman lafiya a matakin ƙasa da ƙasa, mai suna Board of Peace.
Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa sharaɗin samun kujerar dindindin cikinsa shi ne biyan dala biliyan ɗaya daga kowace ƙasa da ke da sha’awar shiga.
An ƙaddamar da kwamitin ne a birnin Davos na Switzerland yayin Taron Tattalin Arziƙin Duniya, tare da shugabannin ƙasashe 19, ciki har da na Argentina da Hungary, waɗanda suka rattaba hannu kan shigarsu.
Trump ya ce an kafa kwamitin ne domin tabbatar da zaman lafiya, musamman a Gaza bayan yaƙin Isra’ila da Hamas, sai dai daga bisani ya faɗaɗa aikinsa zuwa warware rikice-rikice a sassan duniya daban-daban.
Sai dai samar da kwamitin ya janyo cece-kuce, inda wasu ke zargin Trump da shirin yi wa Majalisar Ɗinkin Duniya kishiya, zargin da ya Trump ɗin ya musanta yana mai cewa kwamitin zai yi aiki ne tare da Majalisar Ɗinkin Duniya.
Wani abin da ya ƙara tayar da ƙura shi ne miƙa goron gayyata ga shugaban Rasha, Vladimir Putin, duk da zargin da ake yi masa kan yaƙin Ukraine, da kuma Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, wanda ake tuhuma da aikata laifukan yaƙi a Gaza.
A yayin da Morocco ta zama ƙasa ta farko daga Afirka da ta amince da kwamitin, ƙawayen Amurka irin su Faransa da Birtaniya sun nuna shakku, inda Birtaniya ta ƙauracewa halartar bikin ƙaddamar da shi.
Da yake jawabi a Davos, Trump ya ce yana da cikakken tabbacin shirin zai taimaka wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Gabas ta Tsakiya da sauran sassan duniya.
Aƙalla shugabanni da wakilai daga ƙasashe 20, ciki har da Uzbekistan, Azerbaijan, Turkiyya da wasu ƙasashen yankin Gulf, ne suka sanya hannu kan shirin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link