An tabbatar da kisan Ministan Tsaro da Babban Hafsan Sojojin Iran

[ad_1]



Hukumar dillancin labaran Iran ta IRNA ta tabbatar da cewa babban hafsan sojojin ƙasar, Abdul Rahim Mousavi, da Ministan Tsaro, Aziz Nasirzadeh, na cikin manyan jami’an gwamnatin da suka rasu sakamakon hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila da aka kai wa Iran a ranar Asabar.

Wannan na zuwa ne bayan Iran ta tabbatar da mutuwar Jagoran Addini, Ayatollah Ali Khamenei, tare da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Ali Shamkhani, da kuma babban kwamandan IRGC, Mohammad Pakpour.

IRNA ta ce akwai ƙarin manyan kwamandojin rundunonin tsaron ƙasar da aka kashe a hare-haren, kuma nan gaba kaɗan za a bayyana sunayensu.

Hukumomi a Iran sun tabbatar da cewa harin da aka kai da sanyin safiyar Asabar , ya yi ajalin Khamenei a yayin da yake ofishinsa a birnin Tehran.

Haka kuma, kafofin watsa labaran ƙasar sun ruwaito cewa an kashe ‘yar Ayatollah Ali Khamenei da jikarsa da kuma surukinsa a harin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *