HOTUNA: Dubban mutane na alhinin kisan Khamenei a Iran
Dubban mutane sun hallara a wasu manyan biranen Iran a safiyar wannan Lahadin nan domin jimamin rasuwar Jagoran Addini na ƙasar, Ali Ayatollah Khamenei.
Masu makokin waɗanda galibi ke sanye da baƙaƙen kaya, sun cika Dandalin Enghelab inda suke rera waƙen “mutuwa ta tabbata kan Amurka da Isra’ila”, yayin da da dama ke ɗaga tutocin Iran da hotunan marigayin.
Haka kuma, Al Jazeera ta ruwaito cewa wasu dubban masu makoki sun yi dandazo a tsohon birnin Isfahan domin marigayi Khamenei.
Wani bidiyo da gidan talabijin na gwamnatin Iran, Press TV ya wallafa, ya nuna taron jama’a masu yawa da suka yi dandazo a dandalin Naqsh-e Jahan, suna bayyana jimami da baƙin ciki.
Haka kuma, bidiyon da kamfanin dillancin labarai na Iran, Tasnim, ya wallafa ya nuna dubban mutane suna halartar zaman makokin da aka soma domin girmama marigayin.
A cikin bidiyon, an ga jama’a na bugun kai da ƙirjinsu — wani salo ne da ake amfani da shi wajen nuna alhini da makoki a Iran.
Haka nan kuma, an ruwaito irin waɗannan al’amura a lardin Lorestan, a cewar jaridar Tehran Times.
Tun da safiyar Lahadi ne dai gwamnatin Iran ta tabbatar da rasuwar Khamenei, bayan wani harin haɗin gwiwa na Amurka da Isra’ila da aka kai a Tehran a ranar Asabar.
Gidan talbijin na ƙasar Iran ya sanar da makokin kwana 40 tare da bayar da hutun kwana bakwai, bayan kisan shugaban addinin ƙasar mai shekara 86, wanda ke kan mulki tun shekarar 1989.

Kafofin watsa labaran Iran sun ruwaito cewa an kashe ‘yar Ayatollah Ali Khamenei da jikarsa da kuma surukinsa a harin.
“Shahadar da shugaban addini ya yi ba za ta sa a manta da tafarkinsa da jagorancinsa ba, hasali ma, za a tabbatar da su ne bisa ƙarfin gwiwa da jajircewa,” a cewar mai gabatar da labarai a gidan talbijin na gwamnatin Iran.
Rundunar juyin-juya-hali ta Revolutionary Guards ta sha alwashin yin ramuwar gayya kan “waɗanda suka kashe” Khamenei.
“Rayuwar gayya da ƙasar Iran za ta yi za ta kasance mai tsanani kuma cike da karsashi, sannan waɗanda suka kashe Shugaban Al’umma ba za su ci bulus ba,” in ji wata sanarwa da rundunar juyin-juya-hali ta fitar.