ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya

[ad_1]


Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (ECOWAS), ta musanta iƙirarin da Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi cewa ana kashe Kiristoci a Nijeriya.

A wata sanarwa da ECOWAS ta fitar a ranar Talata, ƙungiyar ta ce kalaman Trump ba su da tushe kuma suna iya haddasa tashin hankali da rikice-rikicen addini a yankin da tuni ke fama da matsalar tsaro.

ECOWAS ta ce hare-haren masu tsattsauran ra’ayi a Afirka ta Yamma ba sa bambance tsakanin Musulmi ko Kirista, domin suna cutar da jama’a baki ɗaya.

Ƙungiyar ta kuma roƙi ƙasashen duniya su tallafa wa gwamnatocin yankin wajen yaƙar ta’addanci, maimakon yaɗa maganganun da za su ƙara raba kan al’umma.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *