Gwamnatin Kano ta kaddamar da dakarun tsaron al’umma 2,000
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rundunar tsaro mai dakaru 2,000 domin aikin kare al’umma a matakin unguwanni a fadin jihar.
A safiyar Talatar nan gwamnatin ta kaddamar da dakarun rundunar, wadda ta ƙunshi matasa da aka kammala ba wa horo na musamman kan ayyukan tsaro.
Dakarun rundunar sun kwashe watanni suna samun horo a fannin tsaro da suka kunshi tattara bayanan sirri da dangoginsu da kuma aiki tare da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro.
An kaddamar da dakarun ne a daidai lokacin da jihar ke fama da matsalolin tsaro da suka shafi ayyukan daba, kwacen waya, shaye-shaye da kuma ayyukan ’yan bindiga a baya-bayan nan.
Kafa rundunar na da nufin ganin jami’anta suna taimaka wa jami’an tsaro na ƙasa wajen sa ido da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a matakin unguwanni, a matsayin wani mataki na ƙarfafa tsaro da rage laifuka a sassan jihar.
Gwamnatin Kano ta ce za a girke jami’an sabuwar rundunar a kowacce daga cikin ƙananan hukumomi 44 da ke Jihar domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a kasuwanni da makarantun da unguwanni da sauran muhimman wurare.
Ta jaddada cewa kafa rundunar zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya da kuma bai wa al’umma kwarin gwiwar rayuwa cikin aminci, tana mai kira ga al’ummar jihar da su ba wa jami’an rundunar hadin kwai domin samun sana a wannan aiki da aka sanya a gaba na samar da tsaron rayuka da dukiyoyi.