‘Yansanda Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Fashi A Kano
‘Yansanda a Jihar Kano sun kama wani ƙasurgumin ɗan fashi da makami, Abba Aliyu, wanda aka fi sani da Abba Fiya, bayan sun amsa kiran gaggawa a unguwar Hausawa.
An kama shi ne a ranar Lahadi, yana da shekaru 26, ɗan asalin unguwar Dala.
An samu wuƙa a hannunsa.
‘Yansanda sun ce ya amsa laifin aikata fashi da makami da rikice-rikicen ƙungiyoyi a Kano da wasu jihohi kamar Ribas da Legas.
Rundunar ta ce tana gudanar da bincike, kuma za ta gurfanar da shi a gaban kotu.
‘Yansanda sun yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin saboda saurin amsa kiran da kuma yadda suka tafiyar da lamarin cikin ƙwarewa.
Sun ce irin wannan aiki yana taimakawa wajen tabbatar da tsaro a al’umma da rage aikata laifuka.
Hakazalika, hukumomi sun buƙaci mazauna jihar su kasance masu lura da kuma bada rahoton duk wani abin da ya shafi ayyukan tsaro ga ‘yansanda.
Za a iya tuntubar ofishin ‘yansanda mafi kusa ko a kira layukan agajin gaggawa 08032419754, 08123821575, 09029292926, ko amfani da manhajar Rescue Me ta NPF.