Abubuwan Da Ya Kamata A Lura Da Su Kafin Fara Kiwon Agwagwa (Geese)
[ad_1]
Agwagwar Gis na daga cikin sahun dangin tsintsaye da suke yin Ƙwai, inda kuma waɗanda suke kiwata su ke samar wa da kawunansu kuɗaɗen shiga.
Sanya Masu Maniyyin Macen Gis: Ana ɗaukar maniyyin macen Gis a saka wa wasu dangin tsintsaye, domin a samar da nau’i na Gis, musamman domin su ƙyanƙyashe su a samu Ƴan tsaki, don kiwatawa.
- Gwamnatin Jihar Gombe Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasar New Zealand Kan Kiwon Dabbobi
- Tawaga Ta 26 Ta Jami’an Kiwon Lafiyar Sin Ta Isa Rwanda
Nau’ikan Naman Gis: Agwagwar Gis ta kasance tana da nau’ikan Nama biyu, inda kuma take ɗauke sinadarin protein, inda kuma masu kiwonta ke samun kuɗaɗen shiga.
Jurewa Sauyin Yanayi: Agwagwar Gis na jurewa kowane irin sauyin yanayi, ba su cika damuwa da sai an kula da su ba, sai dai, ana buƙatar mai kiwata su ya ksance ba ya yin wasa da ba su abinci.
Tanadar Ɗakin Kwana: Ana son wanda yake kiwata su, ya tabbatar da ya tanadar musu da ɗakin kwana, wanda kuma zai kasance an yi shi a wadace, domin su wataya yadda ya kamata.
Sun kuma kasance masu buƙatar ruwa, tu’ammali da ruwa a koda-yaushe, a sabobda haka, ya zama wajbi ga mai kiwata su, ya tabbatar da an samar musu da wadataccen ruwan sha.
Ciyar Da Su: Sun fi cin Ciyawa da kuma saurin nau’ikan abinci, za ka kuma iya ciyar da su da Alkama, musamman ganin tana da saurin taunuwa a wurinsu.
Gis na kai wa tsawon shekaru tana rayuwa, inda aƙalla take kai wa daga shekara 20 zuwa 30, suna kuma fara yin ƙyanƙyasa ne daga watan Satumba zuwa watan Okutoba.
An jima ana kiwon sa a ƙasar nan, musamman a loakcin da mutane suka ankara cewa, ana kiwata shi kamar yadda ake kiwata Talo-talo da Kaji da kuma sauran tsintsaye.
Har ila yau, kiwata shi ana samun ɗimbin kuɗaɗen shiga masu yawa ga waɗanda suka rungumi fannin, musaman aƙasar nan.
Gis sun kuma kasance dangi na Agwagi sai dai, yadda ake kiwata su da Agwagi akwai ban banci.
Ana samun ɗimbin damammaki a kiwon Gis, waɗanda suka haɗa da samun ƙwai, nama da kuma sinadaran gina jiki kamar su protein, haka ana sarrafa Gashinsa zuwa yin suttura da sauransu.
Gis na taimaka wa manoma wajen cinye Ciyarwar da ta fito a gonakinsu, inda daga lokaci zuwa lokaci sukan cinye Ciyawar da ke gonar.
Suna kuma jure wa harin sauran dabbobin, haka suna da saurin tuna abu, inda kuma yawan ƙarar da suke yi, kan taimaka wajen samar da tsaro ga masu kiwata su a gida.
Wata babbar matsala da ke tattare da kiwata su ita ce, suna da yawan ƙara wacce ba za ka iya jure mata ba.
Ba su da wuyar kiwo, sannan kuma suna da saurin girma, musaman idan ana samar musu da abinci a kan lokaci.
Yana samar da nama da kuma ƙwai masu lafiya da gina jikin ɗan’adam, kuma Gis na bijire wa kamuwa daga cututtuka da kamuwa da cutar murar tsntsaye.
[ad_2]
Source link