Matashin da ya kashe uwa da ’ya’yanta ba shi da amfani a cikin al’umma — Mahaifinsa
[ad_1]
Mahaifin ɗaya daga cikin matasan nan uku da ake zargi da kisan mutane bakwai a unguwar Ɗorayi Charanci da ke ƙwaryar birnin Kano, ya buƙaci hukumomi su gaggauta zartar masa da hukunci.
Malam Auwal, wanda ya zanta da gidan rediyom Freedom, ya sanar da barranta kansa da ɗan nasa, yana mai cewa ba shi da wani amfani a cikin al’umma, saboda haka mahukunta su ɗauki matakin zartar masa da hukuncin kisa ba tare da ɓata lokaci ba.
“Ba na son a ɓata lokaci da shari’a. Ya kamata Umar da ire-irensa a kawar da su gaba ɗaya. Ko a gidan yari bai dace a ɗaure su a riƙa ciyar da su da kuɗin harajin jama’a ba,” inji shi.
Mahaifin ya yaba wa ’yan sanda bisa yadda suka ɗauki mataki kan lamarin cikin gaggawa, yana mai cewa ya riga ya sallama ɗan nasa, tare da cewa hatta zaman kotun da za a yi yayin shari’ar shi da mahaifiyar Umar ba za su halarta ba.
Aminiya ta ruwaito cewa, tuni dai rundunar ’yan sandan Kano ta kama, Umar Auwal, jigo cikin matasan nan uku da ake zargi da kashe Fatima Abubakar da ’ya’yanta shi da tsakar ranar Asabar.
Rundunar ’yan sandan ta kuma tabbatar da cewa wanda ake zargin ya amsa laifin aikata kisan, tare da amincewa da hannu a wani hari da aka kai a unguwar Tudun Yola, inda aka kashe matan aure biyu sannan aka banka wa gidansu wuta.
Yadda aka kama ababen zargin
A ranar Lahadin da ta gabata ne rundunar ’yan sandan Kano ta sanar da kama ababen zargin uku bisa wani aikin tattara bayanan sirri da aka gudanar wanda Sufeto Janar na ’Yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun ya umarta.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce aikin cafke ababen zargin wanda aka yi ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ’Yan sanda Ibrahim Adamu Bakori, ya gudana da ƙarfe 10 na dare a ranar 17 ga watan Janairu, zuwa ƙarfe 4 na asubahin ranar 18 ga watan Janairu.
Daga cikin matasa da aka kama kamar yadda SP Kiyawa ya wassafa sun haɗa da Umar Auwalu mai shekaru 23 mazaunin unguwar Sabuwar Gandu.
Sauran sun haɗa da Isyaku Yakubu wanda aka fi sani da Chebe mazaunin unguwar Sagagi mai shekaru 40, da kuma Yakubu Abdulaziz wanda aka fi sani da Wawo mai shekaru 21 da ke zaune a yankin Sabon Gida a unguwar Sharaɗa.
Wasu daga cikin kayayyakin da aka samu yayin cafke ababen zargin sun haɗa da wayoyin hannu biyu na waɗanda aka kashe.
Sanarwar ta ce za a miƙa ababen zargin a gaban kuliya da zarar bincike ya kammala.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link