Ƴan Nijeriya Sun Cire Tiriliyan ₦36.3 Ta ATM Cikin Watanni 6 Duk Da Ƙarin Kuɗin Caji — CBN

[ad_1]

Ƴan Nijeriya sun cire jimillar tiriliyan ₦36.34 ta na’urorin ATM tsakanin watan Janairu zuwa Yuni 2025, duk da ƙarin kuɗin caji da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanya domin rage yawan amfani da kuɗi a hannu. Bayanai daga rahoton ƙididdigar bankin sun nuna cewa adadin kuɗin da aka cire ya kusan ninkawa sau uku idan aka kwatanta da tiriliyan ₦12.21 da aka cire a daidai wannan lokaci a shekarar 2024, abin da ke nuna ci gaba da dogaro da kuɗi a hannu a ƙasar.

Wannan ƙaruwar ta biyo bayan sauya tsarin cajin ATM da CBN ya yi a watan Maris, inda ya cire rangwamen damar cire kuɗi kyauta sau uku a wata daga ATM na wasu bankuna, tare da ƙara kuɗin caji. A karkashin sabon tsarin, kwastomomi na biyan ₦100 kan duk ₦20,000 da suka cire daga ATM na wani banki, yayin da ATM da ke waje (offsite) ke iya janyo ƙarin caji har zuwa ₦500 a kowace mu’amala.

  • Tasirin Sabbin Manufofin Kudi Na Babban Bankin Nijeriya (CBN)
  • CBN Ya Tura Dala Miliyan 50 Don Ƙarfafa Kasuwar Musayar Kuɗaɗe

Duk da waɗannan ƙarin kuɗaɗen, adadin cire kuɗi ya ci gaba da ƙaruwa a kowane zangon. A zangon farko na 2025 kaɗai, an cire tiriliyan ₦15.97, kusan ninki uku na ₦5.46 tiriliyan da aka cire a zangon farko na 2024. A zangon na biyu kuma, adadin ya tashi zuwa tiriliyan ₦20.36 tiriliyan. Jimillar yawan mu’amaloli ta kai kusan sau miliyan 858.8, da ƙaruwar kusan kashi 73 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Kungiyoyin ƙwadago da na kare haƙƙin jama’a sun soki ƙarin kuɗin cajin, suna kiran sa da ƙarin nauyi ne ga talakawa. Sai dai wasu masu ruwa da tsaki a ɓangaren bankuna sun ce karin ya zama dole sakamakon hauhawar kuɗin aiki. Duk da haka, bayanan sun nuna cewa ƴan Nijeriya har yanzu na fifita kuɗi a hannu, duk da ƙaruwar hanyoyin biyan kuɗi ta lantarki kamar POS da sauran tsarin zamani.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *