Gwamnatin Kano Zata Kashe Biliyan ₦8.53bn Wajen Aiwatar Da Wasu Aiyuka
[ad_1]
Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da kashe kimanin naira biliyan 8.53 domin aiwatar da manyan ayyukan gine-gine, lafiya, ilimi, samar da ruwan sha da jin dadin jama’a a sassa daban-daban na jihar. An yanke shawarar ne a taron Majalisar na 37 da aka gudanar a ranar Alhamis, 16 ga Janairu, 2026, a gidan gwamnatin Malam Aminu Kano House da ke Asokoro, Abuja.
Da yake yi wa manema labarai bayani bayan taron, Kwamishinan yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce kuɗaɗen sun shafi ma’aikatun gwamnati, hukumomi da sassa daban-daban, tare da nufin magance manyan ƙalubale a fannonin ruwan sha, da kiwon lafiya, da hanyoyi da ayyukan jin daɗin jama’a a faɗin jihar.
- Asiri Ya Tonu: Yadda Aka Kashe Uwa da Ƴaƴanta Shida A Kano
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 3 Da Ake Zargi Da Kisan Wata Mata Da ‘Ya’yanta 6 A Kano
A cewarsa, Majalisar ta amince da kashe Naira biliyan 3.1 domin sayen sinadarin tsaftace ruwa (alum) na tsawon watanni shida a shekarar 2026 ƙarƙashin Ma’aikatar Albarkatun Ruwa.
Haka kuma, an amince da Naira biliyan 1.7 domin gina hanyar mota daga Chiromawa zuwa Garun Babba a ƙaramar hukumar Garun Malam, tare da Naira miliyan 677.5 domin gyara da sake farfaɗowa da Asibitin Rogo bayan gobarar da ta afka masa.
Sauran kuɗaɗen da aka amince da su sun haɗa da Naira miliyan 520 domin sayen na’urar CT Scan a Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase, da Naira miliyan 660.3 domin aikin magudanan ruwa da shimfida tayal a unguwar Ayagi-Aisami da ke ƙaramar hukumar Dala.
Majalisar ta kuma amince da gina masaukin marayu a Gidan Yara na Nassarawa, da gyaran makarantar GJSS Tatsawarki a Kumbotso, da biyan diyya ga manoma da kadarorin da ayyukan hanyoyi da dam-dam suka shafa, tare da yin Allah-wadai da mutuwar wata mara lafiya a Cibiyar Urology ta Abubakar Imam, tana mai jaddada cewa za a ci gaba da bincike har sai an kai ga ƙarshe.
[ad_2]
Source link