’Yan Ta’adda Ba Su Da Mafaka A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa


Babban Hafsan Sojin Ƙasan Nijeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ce ’yan ta’adda, ’yan bindiga da sauran masu aikata laifi ba za su da wajen ɓuya a ko ina cikin ƙasar nan.

Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga jami’ai da sojojin Rundunar Sojin Ƙasa ta Division 2 a Ibadan, a yayin wata ziyarar aiki.

  • An Kama Mata 2 Bisa Zargin Shigar Da Miyagun Ƙwayoyi Gidan Gyaran Hali Na Kano
  • Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Ya ce sojoji za su bi ’yan ta’adda duk inda suke a dazuka, duwatsu da wuraren shaƙatawa domin tarwatsa su.

Babban Hafsan ya ce a baya masu laifi suna amfani da wurare masu wahalar zuwa wajen kai hare-hare kan jama’a, amma daga yanzu sojoji ba za su bari hakan ya ci gaba da faruwa ba.

Ya ƙara da cewa an umarci sojoji su ƙara ayyukan dare da kuma tsarw muhimman wurare domin rage motsin ’yan bindiga.

Ya kuma bayyana cewa an bayar da umarni na kawar da dukkanin ’yan ta’adda daga wurare kamar Gandun Dajin Kainji, Gandun Dajin Old Oyo, da wasu sassan Jihar Kwara.

Ya ce rundunar soji na da ƙudirin dawo da zaman lafiya da kare al’umma a waɗannan yankuna.

Laftanar Janar Shaibu ya yaba da ƙoƙarin kwamandoji da sojoji kan nasarorin da suka samu, tare da buƙatar jami’ai su ci gaba da jajircewa.

Ya kuma tabbatar wa sojoji cewa jin daɗinsu na daga cikin manyan abubuwan da ake bai wa muhimmanci, inda ya ce za a gina sabbin bariki kuma za a biya duk haƙƙoƙinsu a kan lokaci domin ƙara musu ƙwarin gwiwa.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *