Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Kolin CELAC Karo Na 10
[ad_1]
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga taron koli na 10 na Kungiyar Kasashen Latin Amurka da Caribbean (CELAC), wanda aka bude jiya Asabar a Bogota, babban birnin kasar Colombia.
Xi ya ce tun bayan kafuwarta, CELAC ta kasance mai jajircewa wajen inganta zaman lafiya, kwanciyar hankali, ci gaba da wadata a yankin Latin Amurka da Caribbean (LAC), tare da kara sabon kuzari ga hadin kai, hadin gwiwa da ci gaba na bai-daya ga kasashe masu tasowa.
Ya ce a bara, an gudanar da taron ministoci na hudu na dandalin Sin da CELAC cikin nasara a watan Mayu a birnin Beijing, inda ya halarci bikin budewa tare da sanar da cewa Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean za su yi hadin gwiwar kaddamar da shirye-shirye guda biyar da suka shafi hadin kai, ci gaba, wayewar kai, zaman lafiya da mu’amalar al’umma, wanda ya samu karbuwa daga kasashen Latin Amurka da Caribbean.
Kazalika, shugaba Xi ya ce, a cikin shekarar da ta gabata, Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean sun yi aiki tare sosai, inda suke inganta aiwatar da shirye-shiryen guda biyar cikin tsari mai dorewa tare da samar da fa’idodi na ainihi ga al’ummomin bangarorin biyu.
Xi ya jaddada cewa Sin za ta ci gaba da kasancewa abokiya tagari kuma kyakkyawar abokiyar hadin gwiwa ga kasashen Latin Amurka da Caribbean, kana za ta goyi bayansu wajen kare ikon mulkin kansu, da tsaro da kuma muradun ci gabansu.
Ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasashen na Latin Amurka da Caribbean don tabbatar da adalci da gaskiya a duniya, tare da yin hadin gwiwa wajen rubuta sabon babi na gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link