Kasar Sin Na Fatan Inganta Raya Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ta Bai Daya Ga Sin Da Afirka
[ad_1]
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian ya sanar a yau Juma’a cewa, bisa gayyatar da mataimakin shugaban Kenya Kithure Kindiki da mataimakin shugaban Afirka ta Kudu Paul Mashatile da mataimakin shugaban Seychelles Sebastien Pillay suka yi masa, mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng zai kai ziyarar aiki kasashen Kenya da Afirka ta Kudu da Seychelles daga ranar 22 zuwa 30 ga Maris.
Game da batun, Lin Jian ya kara bayyana cewa, shekarar 2026 ita ce shekara ta farko ta aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 15, kuma a ciki ake cika shekaru 70 da fara kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kasashen Afirka, haka kuma ita ce “Shekarar Cudanyar Jama’a da Musanyar Al’adu tsakanin Sin da Afirka”. Kuma wannan ziyarar wata muhimmiyar mu’amala ce tsakanin manyan shugabannin bangarorin biyu. A cewar kakakin, kasar Sin na fatan ganin cewa, ta hanyar wannan ziyara, za ta kara hada shirinta na shekaru biyar-biyar da dabarun ci gaban kasashen uku, da karfafa aminci da juna a fannin siyasa tsakaninta da kasashen uku, da kuma fadada hakikanin hadin gwiwa a fannoni daban-daban, ta yadda za a inganta raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga Sin da Afirka a ko da yaushe cikin ko wane yanayi a sabon zamani. (Mai fassara Bilkisu Xin)
[ad_2]
Source link