Yadda ADC Ta Shiga Gaban PDP Wajen Zama Babbar Jam’iyyar Adawa A Zauren Majalisar Dattawa
[ad_1]
Abin da ya faru ranar Alhamis, 12 ga Maris ya sauya alkablar, inda ‘yan majalisar Dattawa tara masu rike da mukami a majalisar dattawa ta 10 suka bar jam’iyyun siyasarsu zuwa jam’iyyar ADC.
Kamar dai kowacce zaman taron majalisar dattawa da ke gudana, amma a wannan zama ya sauya al’amura lokacin da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya fara karanta wasikun sauya sheka daya bayan daya.
- Sarkin Musulmi Ya Bukaci A Sauya Fasalin Tsarin Tsaro A Yaki Da Ta’addanci
- Rawar Da Sashen Ayyukan Hidimomi Da Biyan Bukatu Ke Kara Takawa A Kasar Sin
‘Yan majalisar dattawan da suka sauya sheka sun hada da Sanata Aminu Tambuwal, daga mazabar Sakwato ta kudu da Enyinnaya Abaribe, a mazabar Abiya ta kudu da Binos Yaroe, a mazabar Adamawa ta kudu da Bictor Umeh, a mazabar Anambra ta tsakiya da Tony Nwoye, a mazabar Anambra ta arewa da Lawal Usman, a mazabar Kaduna ta tsakiya da Ogoshi Onawo, a mazabar Nasarawa ta kudu da Austin Akobundu, a mazabar Abiya ta tsakiya da Ireti Kingibe, a mazabar Babban Birnin Tarayya Abuja.
Bisa ga wannan, Abaribe da Tambuwal da wasu sun shiga jam’iyyar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Dabid Mark ke jagoranta, tare da jaruman siyasa kamar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, da sauran su, domin takarar shugaban kasa a 2027 da kuma gudanar da ingantaccen adawa.
Zaben shugaban kasa na 2027 shi ma zai gudana a wannan al’amari na adawa, musamman a lokacin da ‘yan ADC ke haduwa domin shirya kawar da Shugaban kasa, Bola Tinubu daga kan mulki.
Haka kuma Sanata Seriake Dickson, na mazabar Bayelsa ta yamma ya sanar da matsayinsa na shiga ADC ba, amma zuwa sabuwar jam’iyyar Nigeria Democratic Congress, NDC inda shi ne wanda ya kafa kuma Shugaban Kasa.
Guguwar sauya sheka ta sa ADC ta zama babban jam’iyyar adawa a majalisar dattawa da sanatoci 9, ta ragewa PDP zuwa 6, yayin da APGA ta kasance tana da 1, NNPP 1, NDC 1 da Accord 1, wanda idan aka hada da sanatoci 87 da APC ke da su, ya kai guda 106.
[ad_2]
Source link