An kama uba da ɗansa kan yi wa ’yar shekara 13 fyaɗe a Gombe

[ad_1]



Jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC) sun cafke wani mutum mai shekaru 48, Ibrahim Haruna, tare da ɗansa mai shekaru 15, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyaɗe a unguwar Jekadafari da ke Jihar Gombe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an gabatar da waɗanda ake zargin ne a hedikwatar hukumar a ranar Litinin.

Mai magana da yawun hukumar a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya ce bisa binciken da suka gudanar, uban da ɗan sun aikata laifin ne a lokuta daban-daban.

A cewarsa, Ibrahim Haruna wanda tela ne ya yi aika-aika ne a shagonsa na ɗinki, yayin da ɗansa kuma ya aikata laifin a cikin gidan da suke zaune.

“Mun kammala binciken da muke gudanarwa, kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci,” in ji Sa’ad.

Sai dai Ibrahim Haruna, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, ya musanta zargin, inda ya bayyana cewa kawai ya taɓa yarinyar ya yi a cikin wasa, amma bai yi mata fyaɗe ba.

Hukumar ta ɓoye sunan yarinyar da abin ya shafa don kare mutuncinta da kuma ƙa’idojin kare haƙƙin yara da dokokin kare ‘yancin ɗan Adam suka tanadar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *