Hatsarin mota ya kashe fasinjoji 10 a Filato

[ad_1]



Aƙalla fasinjoji 10 sun mutu, wasu da dama suka jikkata a wani hatsarin mota kan hanyar Jos-Bauchi, a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa da kw Jihar Filato.

Hatsarin ya haɗa da manyan motoci biyu da kuma ƙananan motoci biyu, da misalin ƙarfe 12:12 na tsakar dare kafin wayewar garin Talata, bayan wani shingen sojoji.

Kakakin Hukumar Kiyaye Hadurra ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Filato, Peter Y. Longsan, ya bayyana cewa an gudanar da aikin ceto tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar, ’yan sanda, ma’aikata da mazauna yankin.

“Hatsarin ya haɗa da manyan motoci biyu da ƙananan motoci biyu (Ford Galaxy). Mutane 19 ne hatsarin ya rutsa da su – maza 17 da mata 2.

“Fasinjoji 10, dukkansu maza, sun mutu a wurin, aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Gwamnati Miyabarkate da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), da Asibitin Musamman na Jihar Plateau domin kulawa.”

Ya ƙara da cewa an kai gawarwaki takwas  Asibitin Ƙwararru na Filato da Asibitin Koyarwa na Bingham, yayin da jami’an Ƙungiyar Direbobi (NURTW) suka karɓi gawarwaki biyu domin binne su.

Longsan ya bayyana cewa bincike na ci gaba, sai dai sakamakon farko ya nuna gudu fiye da kima da kuma sakaci wajen tuƙi ne suka janyo hatsarin.

Hukumar FRSC ta yi kira ga direbobi da su guji yin tafiya da dare, su kauce wa gudu da tuƙi cikin haɗari, tare da ɗaukar tsaron rayuwarsu da muhimmanci.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa wannan hatsari ya auku ne cikin kwanaki 12 bayan wani mummunan hatsari da ya yi sanadiyyar mutuwar daliban Jami’ar Jos tara a kan hanyar Zaria.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *