An Gabatar Da Sanarwar Taro Na 5 Na Hukumar Koli Mai Sa Ido Kan Tabbatar Da Da’a Ta JKS Karo Na 20
An gudanar da taro na 5 na hukumar koli mai sa ido kan tabbatar da da’a ta jam’iyyar Kwaminis ta Sin wato JKS karo na 20, daga ranar 12 zuwa yau 14 ga wannan wata a birnin Beijing. Kuma bayan taron, an gabatar da sanarwar da ta bayyana cewa, ya kamata a sa kaimi ga inganta karfin jam’iyyar a dukkan fannoni, da ci gaba da yaki da cin hanci bisa fahimta da jajircewa, ta yadda za a samar da tabbaci mai karfi na cimma burika da ayyukan dake kunshe cikin shirin raya kasa na shekaru biyar biyar, daga shekarar 2026 zuwa ta 2030.
Taron ya gabatar da manyan ayyukan da za a gudanar, na farko shi ne kara sa ido ga harkokin siyasa don sa kaimi ga cimma shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 15, na biyu shi ne sa kaimi ga yaki da cin hanci, da bin matakin da ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS ta dauka mai kunshe da batutuwa takwas na kyautata dabi’a, na uku a yi kokari wajen tabbatar da jami’ai ba su yi amfani da mukamansu ko damar da suke da ita har su yi tunanin karbar cin hanci ba, na hudu shi ne aiwatar da ayyuka bisa doka don biyan bukatun jama’a, na biyar shi ne kara sa ido kan harkokin hukumomin kasar, na shida kuwa shi ne tabbatar da aiwatar da ayyukan sashen sa ido na kwamitin ladabtarwa bisa dokoki. (Zainab Zhang)