’Yan bindiga sun sace shugaban malamai da wasu a Zamfara
[ad_1]
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun tare hanyar Gusau zuwa Gummi a Jihar Zamfara, inda suka sace mutane da dama.
Wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun tare motoci sannan suka yi awon gava da fasinjojin da ke ciki.
Wani shaida ya ce ’yan bindigar sun ɗauki lokaci suna sharafinsu kafin daga bisani suka tafi da mutanen da suka kama.
Daga cikin waɗanda suka sace akwai Malam Sadis Isa, shugaban Majalisar Malamai ta Ƙaramar Hukumar Gummi, abin da ya jefa al’umma cikin tsoro da damuwa.
“Da yammacin ranar Talata, ’yan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa Gummi, sun sace fasinjoji da dama ciki har da Malam Sadis Isa,” in ji shaidar.
Ya ce har yanzu ba a ji daga wajen maharan game da kuɗin fansar mutanen ba.
Mutanen Gummi dai sun daɗe suna fama da hare-haren ’yan bindiga, wanda hakan ya sa da dama daga cikinsu ke guje wa amfani da hanyar Anka zuwa Gusau saboda tsoro.
A baya-bayan nan ma, ’yan bindiga sun kai hari yankin Tsauni da ke Gusau, inda suka sace kansiloli biyu da wani limami bayan idar d sallar Magariba.
A yanzu haka, maharan sun mayar da hankali kan sace matafiya da manoma domin karɓar kuɗin fansa a jihohin Zamfara da Sakkwato.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link