Gwamnatin Kuros Riba ta bankaɗo ma’aikatan bogi 800

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Kuros Riba, ta ce ta gano ma’aikatan bogi har guda 800 a wasu ma’aikatun jihar.

Tun da farko, an daɗe ana zargin gwamnatin da ta gabata ƙarƙashin Farfesa Ben Ayade da biyan albashi ga wasu mutane da ba ma’aikatan gwamnati ba, musamman a ƙananan hukumomin jihar.

Kwamishinan ma’aikata ƙananan hukumomi, Darlington Bassey Eyo ne, ya tabbatar da hakan a Kalaba ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa gwamnati ta fara aikin tantance ma’aikata tun farkon shekarar nan, inda ta duba kowace ma’aikata ɗaya bayan ɗaya.

A cewarsa, wannan ne ya sa suka gano ma’aikatan bogi da yawansu ya kai 800.

Eyo, ya nanata cewa gwamnatin Bassey Otu, ta ƙudiri aniyar kawar da ma’aikatan bogi ta hanyar tantance ma’aikatan jihar baki ɗaya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *