Buƙatar Sake Farfaɗo Da Martabar Ɓangaren Shari’ar Nijeriya

[ad_1]

A watan Okutobar 2016 ne, jami’an DSS suka kai same a gidajen Wasu Alƙalan Koton Ƙoli da ke ƙasar nan, inda suka kama su, bisa zargin cin hanci da rashawa.

Wannan samamen, dai, ya janyo tara da ƙura da kuma tabka muhawa, a tsakanin wasu ƴan ƙasa, bisa yadda aka kai samamen, da suke ganin ba a bi ƙa’ida ba.

Bayan ƴan shekaru, batun ya sha ruwa, sai ga dukkan alamau, har yanzu, irin wancan yamuncin, na ci gaba da faruwa.

Wannna na zuwa ne dai, bayan wasu rahotannin da suka fata a kwanan baya na cewa, Alƙalan Manyan Kutuna guda 34, daga cikin 62 da aka zaɓo, sun gaza cin wani gwaji da aka yi masu, na cancanta.

  • Zargin Almundahanar ₦1.35bn: Kotun Ƙoli Za Ta Warware Taƙaddamar EFCC Da Lamiɗo
  • Shari’ar Annabi SAW Ta Fi Ta Sauran Annabawa Sauki (2)

Sai dai, Hukumar da ke sanya ido kan lamurran Shari’a ta ƙasa wato NJC ta ƙaryata waɗannan alƙaluman wanda ta fayyace cewa, an gudanar da yin wannan gwajin ne a hukumar Hukumar Kula da Shari’a ta Tarayya wato FJSC, wanda kuma har zuwa yanzu, ba a cimma wata matsaya ta ƙarshe ba.

Wannan ƙaryatarwar ta hukumar ba ta tabbabatar da haƙiƙanin gaskiya kan wannan batun ba.

Mu a nan, a namu ra’ayin o dai wannan adadin guda 34 ne, ko kuma ƙasa da haka, hakan na nuna cewa, dai, Alƙalan da aka zaɓo ɗin domin yin gwajin akai alamar tambaya kan batun, na ƙimarsu.

Kazalaka, bisa wani bincike da Hukumomin EFCC da NBS, suka gudanar a 2010 tare da tallafawar sashen da ke a Majalisar Ɗinkin Duniya da ke yaƙi da tu’ammali da kayan maye wato UNODC, ya bankaɗo yadda ake zargin wasu Alaƙalai da hannu dumu-dumu, a batun cin hanci da rashawa.

Mutunci da kuma yarda da sashen Shari’a na ƙasar nan dai, ya fara zubewa ne tun 2016 biyo bayan samamen da jami’an na DSS suka kai a gidajen wasu Alƙalan ƙasar.

Tun ma kafin wancan lokacin akwai hujjoji da suka nuna cewa, akwai matsaloli, a ɓangaren Shari’a na ƙasar, domin kuwa bayan fitar da rahohon bincike na Hukumomin EFCC,NBS da kuma UNODC, Hukumar ta NJC, ta ƙaƙabawa sama da Alƙalai 70 takunkumi, saboda samun su da saɓa ƙa’idojin gudanar da aiki, ciki har da na cin hanci da rashawa, inda hakan ya janyo, har aka kori wasu daga cikinsu, wasu aka yi masu ritayar dole wasu kuma aka dakatar da su,

Kudin tsarin mulkin ƙasar nan dai, ya dogara ne kachokam kan umarnin bin doka da oda.

A yayin da ƴan ƙasa ke ganin Alƙalai sune madora na ƙarshe a gare su, domin a bisa ƙa’ida, ba a sansu da nuna wani banbanci ba, amma idan aka samu akasin hakan, hakan ya nuna cewa, ƴan ƙasa, ba za su kuma sake yarda da su ba.

Fannin na Shari’ar ƙasar nan dai, ana jima ana zarginsa da harƙallar cin hanci da rasahawa, musamman yadda ake sauya fari zuwa baƙi na haƙiƙanin gaskiya, wajen yanke hukunci a gaban Kotu.

Duk da dai cewa, Hukumar ta NJC ta hƙiƙance cewa, har zuwa yanzu ba ta ɗauki mataki kan batun Alƙalan da auak yiwa gwajin na ƙima ba, amma dai, hakan ya nuna cewa, ƙimar ta Alƙalan, na ci gaba da zama abin shakku.

Domin wannan abin matuƙar damuwa ne ace, har zuwa yanzu yawana adadin waɗannan Alƙalan, sun sun ƙasa tsallake siraɗin na gwajin. Musamman domin su zama manyan Alƙalai.

Na farko, a ra’ayin mu, akwai matuƙara buƙatar a yi garanbawul a ɓangaren Shari’ar ƙasar kuma dole a gyara tsarin ɗaukar Alƙalai akai a ƙasar, musamman duba da irin ƙarfin ikon da ake bai wa Alƙalan ƙasar, na gudanar da ayyukansu, domin a tabbatar da cewa, ana bin ƙa’ida da kuma tabbatar da ƙima.

Kazalika, ya kama akai-akai a rinƙa binciken yadda Alƙalai ke gudanar da ayyukansu.

Na biyu, dole ne a tsarara bin ƙa’idar aikin tare da kuma ƙarfafa shi, kuma dole ne ƙungiyar Lauyoyi ta ƙasa wato NBA, ta rinƙa yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukomomin domin a rinƙa sanya ido da kuma ƙabawa duk wani Lauya, da ya sɓa ƙa’idar aikin.

Na uku, dole a kare ƙimar yadda ake tantance waɗanda za a naɗa, a matsayin Alƙalai, tare da kuma jin ra’ayoyin ƴan ƙasa, domin gujewa naɗa baragurbin Alƙali, mumamman wanda aka taɓa samun wani ƙorafi daga gun alumma, akansa ko wasu zarge-zarge.

Akwai kuma buƙatar a samar da wadataccen ilimi a ɓangaren na Shari’a tare da kuma smaar da horo kan sanin makamar aiki.

A ƙarshe, dole ne suma Lauyoyi, su rinƙa kalon kasnu a matsayin masu kishin ƙasa, ba kawai gudanar da aikin domin kuɗaɗen da za su samu ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *