Mai faci ya kitsa garkuwa da kansa domin karbar fansar N12m daga ’yan uwansa
[ad_1]
’Yan sanda sun kama wani mai mai faci mai shekaru 34, mai suna Idris Isiaka, wanda ake zargin ya kitsa garkuwa da kansa domin ya karɓi kuɗi daga iyalinsa a jihar Edo.
Wannan ya biyo bayan wani lamari makamancin haka a ranar 13 ga Janairu, inda ’yan sanda suka kama wata yarinya mai shekaru 18, Obehi Odine, wadda ake zargin ta kirkiri sace kanta a Ekpoma domin ta karɓi Naira miliyan 10 daga iyayenta.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, Eno Ikoedem, ya ce wannan sabon lamari ya faru ne a ranar 10 ga Janairu a Emaudo, Ekpoma, karamar hukumar Esan ta Yamma ta jihar.
Ya ce wanda ake zargi tare da abokan aikinsa guda biyu, Mohammed Saliu da Godwin Mohammed, wadanda yanzu ba a same su ba, sun yada labarin sacewar a kafafen sada zumunta, suna neman kudin fansa na Naira miliyan 12.
Mai magana da yawun ’yan sandan ya ce wanda ake zargi ya tsara wannan shirin tare da abokan aikinsa.
A cewarsa, bayan ya ‘sace’ kansa, sai ya shirya yada labarin a kafafen sada zumunta ta hannun wani ɗan jarida.
Ikoedem ya ce abokan aikinsa sun tuntubi iyalin wanda ake zargi a jihar Kogi, suna barazanar cewa za a kashe shi idan ba a biya kudin fansa ba.
Ya ce, “Dan uwansa daga baya ya sayar da kadararsa ya biya wani bangare na kudin fansa, inda wanda ake zargin ya raba da abokan harkallar tasa.
“Wanda ake zargin ya amsa laifin kuma za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike,” in ji Kakakin ’yan sandan.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link