Haƙƙin Ɗan Adam Na Fuskantar Mummunar Barazana A Duniya – Guterres
[ad_1]
Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce haƙƙin ɗan adam na ƙara fuskantar barazana a sassa daban-daban na duniya.
Ya bayyana haka ne yayin jawabi a taron kare haƙƙin ɗan adam a birnin Geneva, inda ya ce wasu shugabanni na amfani da iko wajen take dokoki da kuma cin zarafin jama’a.
- Tinubu Ya Taya APC Murnar Nasara A Zaɓukan Birnin Tarayya, Kano Da Ribas
- Ramadan: Akpabio Ya Bukaci Musulmai Su Yi Addu’a Don Zaman Lafiyar Kasa
Ya ce a wasu wurare ana take haƙƙin ɗan adam a fili, har ma wasu na alfahari da hakan.
Guterres ya kuma nuna damuwa kan halin da fararen hula ke ciki a ƙasashe kamar Sudan, Gaza da Ukraine, yana cewa ofishinsa na fuskantar matsin lamba saboda ragin samun tallafi.
Ya ƙara da cewa Majalisar Ɗinkin Duniya ba za ta amince da duk wani yunƙuri na hana samar da ƙasashe biyu na Isra’ila da Falasɗinu ba, domin wannan na da muhimmanci ga zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
[ad_2]
Source link