Gobara ta yi ta’adi a Kasuwar Fika da ke Yobe
[ad_1]
Wata mummunar gobara da ta tashi a babbar Kasuwar Fika, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Fika a Jihar Yobe, ta lalata shaguna da dama lamarin da ya janyo asarar dukiyoyi masu tarin yawa.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta yi ɓarna mai tsanani a shaguna da rumfunan kasuwar, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin cinikayya da rayuwar ‘yan kasuwar yankin.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Sakataren Gudanarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), Dakta Mohammed Goje, ya ce an tura jami’an hukumar cikin gaggawa zuwa wurin, tare da haɗin gwiwar hukumar kashe gobara, domin daƙile wutar da hana ta yaɗuwa.
“Mun samu rahoton tashin gobara a babbar Kasuwar Fika, kuma nan take muka ɗauki matakin gaggawa tare da haɗin gwiwar hukumar kashe gobara, wadda ta yi aiki tuƙuru har aka shawo kan lamarin,” in ji Goje.
Ya bayyana aukuwar gobarar a matsayin abin tausayi, musamman ganin cewa ta faru ne jim kaɗan bayan da hukumar ta kammala shirye-shiryen tallafa wa waɗanda gobara ta shafa a garin Bukarti da wasu al’ummomi uku a jihar.
“Girman ɓarnar da gobarar ta yi abin damuwa ne matuƙa, domin ta kawo cikas ga harkokin kasuwanci da rayuwar jama’a.
“Muna jajanta wa al’ummar Fika da duk waɗanda wannan mummunan lamari ya shafa,” in ji shi.
Goje ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na tare da mutanen Fika a wannan mawuyacin lokaci, kuma za ta ci gaba da ba da dukkan tallafin da ake buƙata gwargwadon ikon da ake da shi.

Ya kuma bayyana damuwa kan yawaitar aukuwar gobara a ‘yan makonnin nan, yana mai kira ga hukumomin gwamnati da al’umma baki ɗaya da su rungumi matakan kariya, musamman a kasuwanni, gidaje da wuraren taruwar jama’a.
“Yawaitar afkuwar gobara abin firgici ne, kuma wannan yana nuna buƙatar ɗaukar matakan kariya cikin gaggawa.
“Muna kira ga jama’a da su kasance masu taka-tsantsan, su ba da fifiko ga tsaro, tare da hanzarta kai rahoton duk wata buƙata ta gaggawa,” in ji shi.
Ya jaddada cewa asarar matsuguni da dukiya na haifar da mummunar girgizar tattalin arziki, amma da haɗin kai, shiri da lura, ana iya rage haɗari da raɗaɗin ɓarnar.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tantance musabbabin tashin gobarar ba, haka kuma ba a fitar da ƙiyasin adadin asarar da ta haifar ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link