Ministocin Wajen Sin Da Nijeriya Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Diflomasiyya

[ad_1]

A yau Talata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, da takwaransa na Nijeriya Yusuf Maitama Tuggar, sun yi musayar sakonnin taya murna kan cika shekaru 55 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

A cikin sakonsa, Wang, wanda kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar JKS ta Sin, ya ce tun bayan kulla dangantakar diflomasiyya shekaru 55 da suka gabata, duk da sauyesauyen da suke faruwa a yanayin siyasar duniya, Sin da Nijeriya suna ci gaba da goyon baya ga juna tare da tafiya kafada-da-kafada. Ya ce abotar kasashen biyu ta zarce tsaunuka da tekuna, inda ta kafa tushe mai kwari a zukatan al’ummominsu.

Musamman ma, ya yi nuni da cewa tun bayan kafa cikakkiyar dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a shekarar 2024, bangarorin biyu sun zurfafa amincewar siyasa da juna, sun kuma samar da sakamako mai yawa a hadin gwiwar fannoni dabandaban, tare da kusantar juna wajen fitar da daidaitaccen matsayi a harkokin kasa da kasa da na yankuna.

A nasa bangaren, Tuggar ya ce tun bayan kulla dangantakar diflomasiyya, Nijeriya da Sin sun ci gaba da kasancewa cikin kyakkyawar alaka mai amfanar da juna, tare da zurfafa hadin gwiwa a fannoni dabandaban.

Tuggar ya kara da cewa, Nijeriya na daukar Sin a matsayin muhimmiyar kawa ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, kuma tana ci gaba da karfafa mu’amalar diflomasiyyar bangarori biyu tare da binciko sabbin fannoni na hadin gwiwa domin daidaita su da manufofin harkokin waje na kasashen biyu, da kuma inganta ci gaban alakar Nijeriya da Sin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *