Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Zuru

[ad_1]



Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, ta bayyana alhininta game da rasuwar Sarkin Zuru na Jihar Kebbi, Mai Martaba Manjo Janar Muhammadu Sani Sami (mai ritaya) Gomo II, wanda ya rasu yana da shekaru 81.

Shugaban ƙungiyar, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce marigayin jagora ne mai kishin ƙasa, dattijo nagari kuma basarake mai daraja wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa Najeriya hidima.

A cikin sanarwar ta’aziyyar da mai magana da yawunsa, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, gwamnan ya tuna irin rawar da Sarkin ya taka a aikin soja.

Ya ce Sarkin ya taka rawa sosai lokacin da ya yi Gwamnan soja na tsohuwar Jihar Bauchi, inda ya bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.

Ya kuma bayyana yadda marigayin ya yi ƙoƙarin wajen ci gaban masarautar Zuru da kuma ƙarfafa majalisar sarakunan gargajiya ta Arewa.

Ƙungiyar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, masarautar Zuru da al’ummar Jihar Kebbi.

Ta kuma roƙi Allah Ya jikansa, Ya kuma gafarta masa, Ya kuma sanya Aljannatul Firdaus ta zama makomarsa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *