Darussa Daga Ramadan Na 6: Girmama Ni’ima Da Gujewa Almubazzaranci A Ramalana

[ad_1]

A cikin watan Ramalana muna koyon girmama ni’ima ta hanyar da ba ta saɓa da yadda muke rayuwa a sauran watanni ba. Domin lokacin da mutum yake azumi, yana jin ƙimar ruwa idan yana jin ƙishirwa, yana jin darajar abinci idan yunwa ta dame shi. Wannan yanayi yana tasar zuciya daga sakaci zuwa godiya ga Allah Ta’ãlã.

Sau da yawa mutum yana rayuwa cikin ni’imomi amma bai san ƙimarsu ba sai an ɗauke su na ɗan lokaci sai ya gane shayi ruwa ne. Ramalana na koya mana cewa ni’ima ba aba ce da za a yi wasa ko sakaci da ita ba, illa amanar da Allah da Ya ɗora mana. Yunwa da ƙishirwa da muke ɗanɗanawa a azumi suna zama makaranta ta fahimtar wahalar marasa galihu da kuma girman baiwar Allah a gare mu.

  • Darussa Daga Ramadan Na (3)
  • Darussa Daga Ramadan Na (4)

Idan lokacin buɗa-baki ya yi, muna taruruwa kan abinci cikin farin ciki. Amma wannan taruruwa ya kamata ya zama taro ne na godiya, ba taron almubazzaranci ba. Domin girmama ni’ima yana nufin:
1. Tsare ta daga ɓalɓalcewa.
2. Amfani da ita cikin tsari da adalci.
3. Godiya ga Allah a kanta da zuciya da harshe.
4. Nisantar sako-sako da wuce gona da iri.

Allah Maɗaukaki Ya yi gargaɗi a cikin Alƙur’ani cewa: “Ku ci ku sha, amma kada ku yi almubazzaranci. Lalle Allah ba Ya son masu almubazzaranci.” Suratul A’rafi aya ta (31). Wannan aya tana koya mana daidaito. Musulunci ba ya hana mutum ya ji daɗin halal, amma yana hana wuce gona da iri. Ba a hana cin abinci mai daɗi ba, amma an hana ɓata shi. Ba a hana yin liyafa ba, amma an hana nuna isa da alfahari da ni’ima.

Abin takaici, a wasu lokuta na Ramalana, wanda ya zo domin koya mana jin yunwa da tausayi, sai ya koma wata na gasar girke-girke da ɓata abinci. Ana zuba abinci fiye da buƙata, ana zubar da saura ba tare da tunanin marasa galihu ba. Wannan ya sa darasin Ramalana ya ɓace a rayuwar wasu.

Hakikanin girmama ni’ima shi ne ka ci ka ƙoshi, ka tuna da wanda bai samu ba. Ka rage abin da ya wuce buƙatarka, ka raba wa mabuƙata, ka kuma gode wa Allah da ya ba ka. Godiya ba kalma ba ce kawai; aiki ce. Godiya ita ce amfani da ni’ima ta hanyar da ta dace.

Ramalana wata ne na daidaito; daidaito tsakanin ibada da rayuwa, tsakanin jin daɗi da tsoron Allah, tsakanin amfani da ni’ima da kiyaye ta. Idan muka koyi wannan darasi, to bayan Ramalana ma za mu ci gaba da rayuwa cikin tsari, mu nisanci almubazzaranci, mu kuma zama masu kula da duk abin da Allah Ya hore mana.

Allah Ya sa mu zama masu girmama ni’imominSa, masu godiya a fili da a ɓoye, Ya kuma tsare mu daga wuce gona da iri. Amin.

Abu Razina Nuhu Ubale Ibrahim Paki

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *