Za A Wallafa Makalar Shugaba Xi Kan Bunkasa Karfin Samun Kudaden Kasar Sin
Za a wallafa wata makalar da Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC), ya rubuta game da bin hanyar bunkasa samun kudade mai salo irin na kasar Sin da kuma kara karfin kudi na kasar ta Sin a gobe Lahadi.
Makalar ta Xi, wanda har ila yau shi ne shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin soja na tsakiya, za a wallafa ta ce a fitowa ta uku ta mujallar Qiushi a wannan shekarar, wadda babbar mujalla ce ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar CPC. (Abdulrazaq Yahuza Jere)