Gwamnatin Bauchi Za Ta Haramta Haihuwa Ba A Asibiti Ba
Gwamnatin Jihar Bauchi na duba yiwuwar samar da doka ta musamman domin daƙile ƙaruwar yawan haihuwa a gida, lamarin da ke ƙara jefa lafiyar iyaye mata da jariransu a cikin haɗari.
Bisa alƙaluman da Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNICEF, ya fitar, ya ce kaso uku na mata ne kacal cikin kaso goma ke haihuwa a asibiti wato kaso 31 cikin 100. Yayin da sauran mata kaso bakwai, kwantankwacin kashi 69 cikin 100, su ke haihuwa a gida.
- Xi Da Takwaransa Na Aljeriya Sun Taya Juna Murna Kan Nasarar Harba Tauraron Dan Adam Na Aljeriya
- Sojoji Sun Hallaka Babban Kwamandan ISWAP, Sun Cafke Ƴan Fashi A Borno Da Adamawa
Game da duba lafiyar ciki wato antenatal, cikin mata 100 masu juna biyu, 57 ne suke zuwa antenatal amma daga bisani sukan haihu a gida.
Masu ruwa da tsaki a harƙar kiwon lafiya sun nuna hakan a matsayin abun damuwa matuƙa inda suke kiran da a ɗauki matakin shawo kan hakan cikin hanzari.
Don haka ne ma’aikatar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Bauchi, Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi, shugabannin ƙananan hukumomi da ƙungiyoyin fararen hula suka tsara hanyoyin rage yawaitar mace-macen mata masu juna biyu da jarirai.
Da ya ke jawabi a ranar Asabar a wajen taron tattaunawa na kwanaki biyu kan hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar mace-macen masu juna biyu da jarirai da inganta kiwon lafiya uwa da jarirai, ƙwararren masani kan lafiya na UNICEF, Oluseyi Olosunde, ya ce yana da matukar muhimmanci masu ruwa da tsaki su nemo mafita domin rage mace-macen mata masu juna biyu da yara a jihar.
Ya buƙaci jihar da ta ƙara kasafin kuɗi wajen kula da kiwon lafiya. A cewarsa, alƙaluman da ake da su na buƙatar ɗaukar matakin gaggawa daga masu riƙe da madafun iko a jihar.
Shugaban hukumar kula da lafiyar a matakin farko ta Jihar Bauchi (BSPHDB), Dakta Rilwanu Muhammad, ya ce hukumar ta gano cewa mata da dama suna halartar antenatal amma daga bisani sukan zaɓi haihuwa a gida, lamarin da ke haifar da matsaloli tare da ƙara yawan mace-macen uwa da jariri a jihar.
“Mun yanke shawarar haɗa kowa da kowa, Kakakin Majalisar Dokoki da ’yan majalisa, masu tsara manufofi a ƙananan hukumomi da sauran su, domin duba batun kasafin kudi da sakin kuɗaɗe. Batun mace-macen uwa da jarirai abun damuwarmu ne.”
“A tsawon shekaru, kasafin kuɗinmu ya wuce yadda ma Abuja Declaration ta ayyana na kashi 15 cikin 100 ga lafiya, amma muna ɗaukar ƙarin matakai domin tabbatar da cewa hakan ya haifar da sakamakon mai kyau.
“Ɗaya daga cikin shawarwarin da aka bayar shi ne jihar ta samar da doka da za ta tilasta wa mata halartar antenatal da kuma haihuwa a cibiyoyin lafiya.
“Idan mace ta kasa halartar antenatal ko ta haihu a cibiyar lafiya, ya kamata a hukunta ta, ko ta hanyar tara mai tsauri ko ɗauri a kurkuku, domin tana jefa rayuwar ‘ya’yanta da nata cikin haɗari,” in ji shi.
Hakazalika, Dakta Nuzhat Rafique, babbar jami’ar da ke kula da ofishin UNICEF a Bauchi, ta ce idan aka kafa irin wannan doka, babu wanda zai hana mata zuwa antenatal ko haihuwa a asibiti.
Rafique, wadda ta nuna damuwa kan yawan mace-macen iyaye mata da jarirai a jihar.
Ta bayyana cewa UNICEF na aiki tare da masu ruwa da tsaki a ɓangaren lafiya, shugabannin gargajiya da na addini domin tabbatar da cewa mata sun san irin ayyukan lafiya da ya kamata su samu a lokacin ɗaukar ciki domin haihuwa lafiya, da kuma ayyukan bayan haihuwa wato raino da shayarwa.
Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, ya bayyana rashin jin daɗinsa da waɗannan alƙaluman lafiya, yana mai cewa bayanan suna nuna haƙiƙanin halin da ake ciki a jihar, tare da alwashin ƙarfafa aikin sa ido na majalisar domin tabbatar da cewa ma’aikatu da hukumomin da lamarin ya rataya a wuyansu suna bayar da ingantaccen kulawar lafiya ga jama’a yadda ya dace.