Kisan Gilla: Gwamna ya sauke basarake da wasu a Ebonyi
[ad_1]
Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Ogbonna Nwifuru, ya sauke Basaraken Amasiri tare da dakatar da wasu manyan masu riƙe da muƙamai, biyo bayan kisan gillar da aka yi wa wasu mutum huɗu a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya ɗauki matakin ne saboda zargin cewa wasu sarakuna da kasa ɗaukar matakan kawo ƙarshen rikicin da ya ɓarke, wanda ya kai ga kisan mutane huɗu.
Baya ga sauke basaraken, gwamnan ya kuma dakatar da dukkanin sarakunan gargajiya a yankin Amasiri da ake zargin suna da masaniya kan rikicin.
Haka kuma, ya soke ƙungiyoyin ci gaban al’umma na yankin da kuma soke dukkanin sarauta ko muƙami da gwamnati ta bayar a baya.
Gwamna Nwifuru, ya umarci duk waɗanda wannan mataki ya shafa da su miƙa dukkanin kayan gwamnati da ke hannunsu ga Sakataren Gwamnatin Jihar.
A yayin ziyararsa yankin Edda, inda aka kashe mutanen, gwamnan ya bayyana baƙin cikinsa.
“Abin takaici ne a kashe rayukan mutane ta wannan mummunar hanya. Wannan rashin tausayi ne da rashin tunani.”
Gwamnan ya kuma sha alwashin cewa gwamnati za ta binciko masu hannu a kisan, tare da tabbatar da an hukunta su.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link