Kaduna: Mutum 86 sun ɓace, 80 sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga
[ad_1]
Hakimin ƙauyen Kurmin Wali da ke masarautar Kufana a Ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, Malam Ishaku Dan’azumi, ya bayyana cewa an gano mutum 80 daga cikin waɗanda ake tunanin an sace a ƙauyen kusan makonni biyu da suka wuce.
Sai dai kuma a gefe guda ya tabbatar da cewar har yanzu ba a gano mutum 86 ba.
Aminiya ta ruwaito a baya yadda ’yan bindiga suka kai hari ƙauyen Kurmin Wali, inda suka sace masu ibada daga wasu coci guda uku.
Harin ya fusata jama’a, inda da dama suka yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar an ceto waɗanda aka sace.
Da yake magana kan wannan lamarin, Dan’azumi ya ce mutane 80 sun tsere zuwa cikin daji a lokacin harin, inda suka ɓuya saboda tsoro.
Wannan ne ya sa suka jinkirta dawowa gida ko tuntuɓar hukumomi.
“Yanzu mun tabbatar da cewa an gano mutanenmu 80 a wurare daban-daban. Sun gudu cikin daji sun ɓuya saboda tsoro tun a ranar da lamarin ya faru,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin waɗanda suka tsere ya tuntuɓi al’ummar ƙauyen bayan wasu kwanaki, inda ya sanar da inda suke, lamarin da ya sa aka tura wakilai don tabbatar da gaskiyar lamarin.
“Ɗaya daga cikinsu ya kira ya faɗa mana inda suke. Mun aika mutane zuwa wajen, kuma sun tabbatar da cewa suna can.
“Sun tsorata ne saboda sun yi zaton abin da ya faru a wani ƙauye wanda ’yan bindiga suka ƙone ƙauyen gaba ɗaya, shi ma ya faru da mu. Shi ya sa ba su tuntuɓe mu da wuri ba,” in ji shi.
Hakimin ƙauyen ya tabbatar da cewa an gano mutane 80 a wurare daban-daban a cikin daji.
Dan’azumi ya ce an sanar da gwamnati game da lamarin, amma tsoro ya hna wasu daga cikin mutanen da aka gano dawowa gida, duk da cewa wasu sun riga sun dawo.
“Mun sanar da gwamnati cewa an gano mutane 80. Suna so mu tara su waje guda, amma tsoro ya hana da yawa daga cikinsu dawowa gida. Duk da haka, mun yi magana da su kuma mun tabbatar da inda suke,” in ji shi.
Aminiya ta ruwaito yadda ’yan bindiga suka kai hari ƙauyen Kurmin Wali a ranar 18 ga watan Janairu, inda suka sace mata, yara da maza 177.
A halin yanzu Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya gudanar da taruka da shugabannin al’umma, sarakunan gargajiya, domin magance matsalar tsaro.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, dangane da gano mutane 80, ya ce rundunar tana ƙoƙarin tattara bayanai kafin fitar da sanarwa a hukumance.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link