Sojoji Sun Kama Manyan Ƙunshin Tabar Wiwi 296 A Jihar Ogun
[ad_1]
A ƙoƙarin tsaftace Jihar Ogun daga masu safarar miyagun ƙwayoyi, dakarun rundunar soji ta ’35 Artillery Brigade’, bisa sahihin bayanan sirri da suka samu kan shirin safarar ƙwayoyi, sun yi nasarar cafke buhunan tabbatar wiwi a jihar.
A wata sanarwa da mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Manjo Idereghi Samuel Akari ya fitar a ranar Litinin, 2 ga watan Maris, 2026 ta bayyana cewa, da misalin ƙarfe 4:30 na asubahin ranar 1 ga Maris 2026, sojojin da ke aiki a hanyar Abeokuta zuwa Igboora, sun bi sahun wani babur marar lamba, inda suka kama manyan kunshe-kunshe 296 na wani abu da aka ɓoye cikin manyan buhuna uku, wanda ake zargin tabar wiwi ce. Wanda ake zargin, ya tsallake ya gudu zuwa cikin daji mai tsananin duhu.
Tuni aka miƙa kayayyakin da aka ƙwato ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen Jihar Ogun, domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.
Har ila yau, rundunar ta tabbatar wa al’ummar Jihar Ogun cewa, Sojojin Nijeriya za su ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyi, tare da ƙarfafa tsaro a duk faɗin jihar domin hana masu aikata laifuka yin ta’asa ba tare da hukunci ba.
[ad_2]
Source link