Mun wadata da makamai da za mu yi yaƙi har abada — Trump

[ad_1]



Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ƙasarsa ta wadata da makaman yaƙi da za a iya amfani da su “har abada”, yana mai jaddada cewa suna da shirin yin nasara a duk wani rikici.

Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta na Truth Social.

Ya yi magana kan abin da ya kira tarin makaman da Amurka ke da su, yana mai cewa za a iya tafiyar da yaƙe-yaƙe na dogon lokaci da su kaɗai.

Ya kuma zargi tsohon shugaban ƙasar, Joe Biden, da bai wa Ukraine makaman Amurka masu ƙarfi da yawa.

A ƙarshen wa’adinsa na mulki, Biden ya amince Ukraine ta yi amfani da makamai masu linzami da ke cin dogon zango irin su ATACMS, waɗanda ke iya kai hari har nisan mil 190, wato kimanin kilomita 300.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *