Ɗan Ganduje Ya Gwangwaje Manoma, Da ‘Yan Kasuwa Da Manyan Kyautata A Kano

[ad_1]

Babban Daraktan Ayyukan Fasaha na Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Karkara (REA), Injiniya Umar Abdullahi Ganduje, ya gwangwaje manoma da kanana da matsakaita kamfanoni (SMEs) da na’urar samar da wutar lantarki daga hasken rana da injinan ban ruwa na noman rani a jihar Kano.

A wani biki da aka gudanar a yammacin ranar Lahadi a Kano, Ganduje ya raba injinan ban ruwa masu amfani da hasken rana ga matasa manoma 120, da kayayyakin samar da wutar lantarki ta hasken rana ga ƙananan kamfanoni da matsakaitan masana’antu (SMEs) 160 a faɗin mazaɓar tarayya ta Dawakin-Tofa, Tofa da Rimin Gado ta Jihar.

  • CBN Ta Amince Wa Bankin Masana’antu Buɗe Sashin Bankin Da Babu Riba
  • Ramadan: Gwamna Uba Sani Ya Yi Kira Ga Malamai Da Su Ƙarfafa Haɗin Kai

Shirin, an tanade shi ne a wani ɓangare na ƙarfafa samar da wutar lantarki, wanda kimanin mutane 280 suka ci gajiyar shirin.

Hakan na ƙunshe ne acikin wata sanarwa da Edwin Olofu, mai taimaka wa tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa (APC), Abdullahi Umar Ganduje, ya sanya wa hannu a ranar Litinin a Abuja.

Da yake jawabi a lokacin taron, Injiniya Ganduje ya ce, an tsara shirin ne don tallafawa matasa maza da mata waɗanda kasuwancinsu ya dogara da wutar lantarki, musamman waɗanda ke cikin yankunan karkara.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *