Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 12 a hanyar Lokoja
[ad_1]
Aƙalla mutum 12 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 18 suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a kusa da ƙauyen Kwaita da ke kan babbar hanyar Abuja–Lokoja.
Hukumar Kare Haddura ta Ƙasa (FRSC) ta ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:16 na yammacin Litinin, inda wata tirelar ɗauke da siminti ta kauce daga hanya ta kife a sakamakon gudu fiye da kima, lamarin da direban ya gaza ikon sarrafa motar.
Kwamandan FRSC reshen Babban Birnin Tarayya, Mista Felix Theman, ya ce wasu fasinjoji da ke zaune a saman buhunan simintin sun maƙale, inda suka mutu nan take bayan kifewar motar kuma ta faɗa rami.
Ya ce jami’an FRSC tare da ’yan sanda da jami’an kula da zirga-zirgar ababen hawa ne suka haɗa kai wajen kwashe simintin kafin a iya fitar da gawarwakin.
“Wasu daga cikin fasinjojin da ke zaune kan simintin sun maƙale, sai bayan jami’an FRSC, ’yan sanda da jami’an zirga-zirga sun kwashe simintin sannan aka fitar da gawarwakinsu,” in ji Theman.
Kwamandan ya bayyana cewa aikin ceto ya gudana ne tare da haɗin gwiwar jami’an FRSC, Sashen Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa (MTD) da ’yan sandan yankin Kwali da ke Abuja.
Ya kuma miƙa sakon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, yana mai Allah-wadai da ɗaukar fasinjoji tare da kaya a tireloli da manyan motoci, yana mai bayyana hakan a matsayin sakacin da ke barazana ga rayuka.
Ya jaddada cewa haɗa fasinjoji da kaya laifi ne mai tsanani a dokar zirga-zirga, wanda ke ƙara tsananta asarar rayuka idan hatsari ya faru.
Theman ya yi gargaɗi direbobin haya da masu motocin kamfanoni cewa FRSC za ta ƙara tsaurara matakan doka kan irin wannan aiki a faɗin ƙasar, inda za a kama tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link