’Yan sanda sun kama kwayoyin N165.4m da makamai a Kano

[ad_1]



’Yan sanda sun kama miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai Naira miliyan 165.4 a watan nan na Satumba a Jihar Kano.

Daga ciki, jami’an rundunar sun kama kwayoyin da kudinsu ya kai Naira miliyan 82.7 a unguwar Rimin Auzinawa, suka mika ga Hukumar Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) domin kammala bincike da gurfanarwa a gaban kuliya.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa rundumar ta kuma kama kwayoyin Tramadol da kudinta ya kai Naira miliyan 60.3 da kwayar Pregabalin ta Naira miliyan 22.4 da kuma sinki 523 na tabar wiwi da injinan tura kudi na POS guda biyar daga hannun wadanda ake zargi a sassan jihar.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa rundunar ta kama mutum 105 da ake zargi da safara miyagun kwayoyin da mallakar miyagun makamai da sauran laifuka.

Daga cikin mutanen, ana zargin 17 da laifin fashi da makami, 8 da zargin dillacin kwayoyi da kuma 9 zargin satar motoic, masu satar babur biyar da ’yan daba 57 da kuma barayi 9.

Ya ce kayan laifin sun hada da bindigogi kirar Ak-47 guda uku, Pistol guda 6, AK-47, da sauran bindigogi kirar gida guda uku, harbi-ruga guda daya da albarusai da takubba da adduna da wukake da Dan-Bida. Sauran sun hada da motoci biyu, A Daidaita Sahu biyu, babura 13 da shanu uku da wasu kayan sata iri-iri.

Ya danganta nasarar da umarbin Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun, na hadin gwiwa da al’umma wajen dakile ayyukan laifi gabanin bukukuwan.

Ya bayyana cewa sashen Operation Kukan Kura da rundunar ta kafa ya taka muhimmiyar rawa wajen takaita ayyukan laifi ta hanyar hadin kan al’ummar gari.

Kwamishinan ya yaba wa al’ummar jihar bisa irin hadin kai da suke ba wa rundunar, wanda ya ce ya taimaka matuka wajen dakile barazanar tsaro daga bata-gari.

Ya kara da kiran su da su ci gaba da taimaka wa rundunar da muhimman bayanai da za su taimaka wajen dorewar nasarar da aka samu kan masu aikata miyagun laifukan.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *