Yanayin kasuwa ne ya sa farashin man fetur ya tashi — NMDPRA

[ad_1]



Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA), ta ce sauyin farashin mai da aka samu a gidajen mai ya samo asali ne da yadda kasuwa ke tafiya a yanzu.

Mai magana da yawun hukumar, George Ene-Ita ne, ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.

Masu ababen hawa da dama a Abuja sun nuna damuwa kan ƙarin farashin man fetur, wanda a baya ake sayarwa tsakanin Naira 875 zuwa Naira 880 kan kowace lita.

A yanzu haka, ’yan kasuwa masu zaman kansu suna sayar da fetur tsakanin Naira 960 zuwa Naira 1,000 ko sama da haka kan kowace lita.

Gidajen mai mallakin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) kuwa suna sayarwa kusan Naira 960 kan kowace lita.

Ene-Ita, ya ce bambancin farashin da ake samu a sassa daban-daban na ƙasar nan ba shi da alaƙa da gwamnati, sai don yanayin kasuwa.

“Najeriya tana amfani da tsarin sayar da man fetur ta hanyar bai wa kasuwa ’yancin gashin kai. Don haka sauyin farashin mai yana faruwa ne saboda yadda kasuwa ke tafiya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa a irin wannan tsarin, farashin mai yana canzawa ne gwargwadon yanayin kasuwa.

Ya kuma bayyana cewa manufar wannan tsari ita ce ƙarfafa gasa tsakanin ’yan kasuwa, inganta aiki, da kuma jawo ƙarin jari a ɓangaren man fetur da iskar gas a Najeriya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *