Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaryata Rufe Makarantu Gaba Ɗaya A Nijeriya

[ad_1]


Kwana guda bayan umarnin rufe manyan makarantun sakandare da gwamnatin tarayya ta yi, ta ƙaryata wani rahoto da ke yawo cewa za a rufe duk makarantu a faɗin Nijeriya daga 24 ga watan Nuwamba, 2025.

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, ta hannun mai magana da yawunta, Folasade Boriowo, ta ce wannan labari da ke yawo a kafafen sada zumunta ƙarya ne kuma bai fito daga kowace hukuma ta gwamnati ba.

An rufe makarantu 41 bayan hukumomin tsaro sun gargaɗi gwamnati game da hare-haren da ke aukuwa a makarantun wasu sannan ƙasar nan.

An umarci shugabannin makarantun da su sallami ɗalibai, ko kuma su ci gaba da yin darusa ta yanar gizo idan akwai hali.

Sai dai Ma’aikatar ta ce babu wani umarni da ya shafi rufe makarantu a faɗin ƙasar.

Boriowo ta roƙi jama’a da suke amfani da bayanan hukumomi kawai, su kuma yi watsi da duk wani saƙo da ba su tabbatar da shi ba, tana mai cewa yaɗa ƙarya, musamman game da tsaron makarantu, na iya haifar da tsoro da rikita matakan tsaro.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *