Rikicin Gabas Ta Tsakiya: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Kwaso ‘Yan Nijeriya Daga Iran

[ad_1]

Gwamnatin Tarayya ta fara kwashe ‘yan Nijeriya da ke zaune a ƙasar Iran waɗanda suka nuna cewa suna son a dawo da su gida.

An fara fitar da su ta kan iyakar Iran zuwa ƙasar Armenia domin tabbatar da tsaron lafiyarsu yayin da rikici ke ci gaba da ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya.

  • Kotu A Norway Ta Ɗaure Ɗan Wasan Nijeriya Kan Zargin Aikata Fyaɗe
  • Saudiyya Ta Rage Samar Da Man Fetur Saboda Matsalar Jigila A Hormuz

Shugabar Hukumar ‘Yan Nijeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa ce, ta bayyana hakan a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, a ranar Talata.

Ta ce kawo yanzu babu wani ɗan Nijeriya da rikicin ya shafa a Iran.

Ta kuma ƙara da cewa jami’an ofishin jakadancin Nijeriya suna kan iyakar Iran da Armenia domin karɓar ‘yan Nijeriya da taimaka musu su tsallaka iyakar zuwa waje mafi aminci.

Dangane da dawo da su gida ta jirgin sama, Dabiri-Erewa ta ce a halin yanzu sararin samaniyar yankin ba shi da tsaro.

Duk da haka, ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya da ke Gabas ta Tsakiya cewa Gwamnatin Tarayya na shirye-shiryen kwaso su da zarar an samu damar hakan.

Ta ce: “Kwanaki biyu da suka wuce an samu jirgi daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa zuwa Legas kafin daga bisani wani hari ya sa aka rufe sararin samaniyar.”

Ta kuma ƙara da cewa: “Da zarar an buɗe sararin samaniyar, tawagar Gwamnatin Tarayya da ta ƙunshi jami’ai daga ma’aikatu daban-daban za su fara aikin kwaso ‘yan Nijeriya zuwa gida.”

Matakin na zuwa ne bayan rikicin da aka fara tun a ranar 28 ga watan Fabrairu, bayan harin da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *