Kwastam ta kama kayan haɗa bam a Kwara
[ad_1]
Hukumar Kwastam a Jihar Kwara, ta kama kayayyaki da dama da ake zargin an shigo da su ba bisa ƙa’ida ba, ciki har da waɗanda ake amfani da su wajen haɗa abubuwan fashewa.
Muƙaddashin Kwantirolan hukumar a jihar, DC Najeem Akanmu Ogundeyi ne, ya bayyana hakan yayin da yake nuna kayayyakin da aka kama a Ilorin.
Ya ce kayayyakin da aka kama sun haɗa da na’urori 222 da ake zargin ana amfani da su wajen haɗa abubuwan fashewa, buhun shinkafar ƙasar waje guda 1,107, motoci 14 da kuma jarkar man fetur guda 317.
Sauran kayayyakin sun haɗa da buhun sinadarin lithium guda 120 da aka haƙo ba bisa ƙa’ida ba, kayayyakin gwanjo, tayoyi da kuma sukari da aka shigo da su daga ƙasashen waje.
Hukumar ta ce jimillar kuɗin harajin kayayyakin ya kai Naira miliyan 478,171,315.
Ogundeyi, ya ce hukumar ta samu nasarar kama kayayyakin ne sakamakon bayanan sirri da kuma haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro.
Ya ce: “Kun san abin da ake yi da waɗannan na’urorin? Duk jami’an tsaro da ke nan sun san ana amfani da su wajen haɗa abubuwan fashewa, shi ya sa muka daƙile shigowarsu.”
Kwanturulan ya kuma ce hana shigo da shinkafa daga waje wata manufa ce ta Gwamnatin Tarayya domin ƙarfafa noma a cikin gida da kuma samar da ayyukan yi.
Ya ƙara da cewa: “Duk da gargaɗin da ake yi akai-akai, wasu na ci gaba da karya dokokin gwamnati. Amma haɗin gwiwar jami’an tsaro da bayanan sirri na taimaka mana wajen daƙile irin waɗannan laifuka.”
Ya kuma buƙaci ’yan kasuwa da al’ummomin da ke kan iyaka su guji yin fasa-ƙauri, su rungumi kasuwanci na gaskiya domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link