Hadurran Kwale-kwale: Al’ummomin Yankunan Na Neman Daukin Gwamnati

[ad_1]

Al’ummar Jihohin Sakkwato da Neja da Kogi da Yobe, sun nemi daukin gwamnatin tarayya, kan yawaitar haduran kwale-kwale, musamman ganin irin yadda yake cin rayukan al’umma lokaci bayan lokaci.

Ana danganta yawancin haduran ne da amfani da kwale-kwale marasa inganci da kuma daukar mutane fiye da kima, a kan haka ne ake ganin hukumomin kula da tafiye-tafiye a ruwa da kuma hukumomin bayar da agaji, su sanya ido tare da hukunta wadanda aka samu da sakaci a afkuwar haduran kwale-kwalen.

  • Sin Ta Ce Ficewar Amurka Daga Hukumomin Kasa Da Kasa 66 Ba Sabon Abu Ba Ne
  • Majalisar Dokokin Legas Ta Amince Da Kasafin Tiriliyan ₦4.4 Na Shekarar 2026

A wani mataki na yunkurin kawo karshen yawaitar mace-mace a magudanan ruwa na Nijeriya, mazauna Karamar Hukumar Nguru da ke Jihar Yobe, sun yi kira ga gwamnatin tarayya; da ta dauki matakin gaggawa na kare ci gaba da afkuwar haduran jiragen ruwa.

Wasu daga cikin mazauna yankin, sun zanta da LEADERSHIP, bayan hadarin da ya afku a yankin, inda suka ce; kimanin mutum 29 ne suka rasa rayukansu a daren ranar Asabar.

Daya daga cikin mazauna yankin, Malam Abubakar Ali, ya bukaci gwamnati da ta tabbatar da cewa; kwale-kwalen da ake amfani da su, suna dauke da injina masu kyau tare kuma da samar da rigunan ceto.

Ya kara da cewa, tilas ne a tilasta wa masu gudanar da aikin, mutunta iyakokin kwale-kwalen da kaucewa yin lodin kaya da kuma yin tafiye-tafiye da daddare.

Daya daga cikin Hakimai, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa; kwale-kwalen, na daukar fasinjoji fiye da kima, wanda hakan ke sanadiyar haifar da hadarurruka daban-daban.

Wani dan kasuwa a garin, mai suna Alhaji Musa Bello, ya bayyna cewa; ya ji takaicin lamarin da ya kusan hallaka iyalansa baki-daya, yana mai bayyana lamarin a matsayin mai matukar radadi tare da ban tausayi.

“Na yi matukar bakin ciki sosai, game da hatsarin jirgin ruwan da ya afku, don haka; akwai bukatar samar da matakai, domin kauce wa sake faruwar wannan hadari a nan gaba,” in ji shi.

A wani labarin kuma, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya kai ziyarar jajanta wa Masarautar Nguru, musamman al’ummar Garbi, a ranar Litinin 5 ga watan Janairun 2026, biyo bayan wani mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Gwamnan, wanda ya jagoranci wata babbar tawaga zuwa Nguru, ya samu wakilcin mataimakinsa, Hon. Idi Barde Gubana.

Buni ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma matukar radadi, inda ya bukaci al’ummar yankin Garbi da Kauyen Adiyani da ke Jihar Jigawa, da su dauki afkuwar a’lamarin a matsayin wani iftila’i daga Allah SWT.

Da yake jajanta wa iyalan wadanda suka mutu, gwamnan ya bayyana cewa; a musulunci, duk wadanda suka mutu ta hanyar nutsewa a ruwa, ana daukarsu a matsayin shahidai (Shaheed), wadanda suke samun rahama ta musamman daga wajen ubangiji, idan aka yi la’akari da irin radadin mutuwar tasu.

Har ila yau, ya yi addu’ar Allah ya ji kan wadanda suka mutun, ya kuma sa Aljanna ce makomarsu.

Gwamnan, ya kuma sanar da bayar da tallafin kudi da ya kai kimanin naira miliyan 20 tare da bayar da naira 500,000 ga iyalan kowannen wadanda suka rasa rayukan nasu, sannan kuma; an bai wa wadanda suka samu raunuka kyautar naira 200,000 kowannensu.

Ya kara da cewa, a yunkurin sake hana afkuwar lamarin a nan gaba, Gwamna Buni, ya umarci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), da ta shirya horo na musamman tare da wayar da kan masu sana’ar ta kwale-kwale a cikin gida, domin kiyaye hadarin da ke tattare da ruwa.

Ya kuma bayyana shirin da gwamnatin jihar ta yi na sayo rigunan ceto da sauran kayayyakin kariya, da kwale-kwalen lantarki na zamani, yayin da ya gargadi masu amfani da su kan yin mummunan lodin kwale-kwale da fasinjoji da sauran kayayyaki.

Shi ma da yake yin nasa jawabin, dan majalisa mai wakiltar Nguru, Machina, Yusufari da Karasuwa, Hon. Tijjani Zannah Zakariyya, tare da Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Alhaji Baba Mallam Wali, ya bukaci al’ummar da abin ya shafa, da su ci gaba da yi wa wadanda suka rasu addu’ar Allah ya gafarta musu da kuma neman lafiya ko ceto wadanda har yanzu ba a gan su ba.

Sakataren zartarwa na Hukumar SEMA, Dakta Mohammed Goje, ya bayyana cewa; lamarin ya faru ne a ranar Asabar 3 ga watan Janairun 2026, inda wani kwale-kwalen da ke dauke da fasinjoji kusan 52, wadanda yawancinsu masunta ne da ‘yan kasuwa daga Kauyen Adiyani da ke Jihar Jigawa zuwa Garbi a Karamar Hukumar Nguru ya kife.

Ya bayyana cewa, an tabbatar da mutuwar mutum 29 tare da ceto mutum 15 da ransu, yayin da takwas kuma suka bace, har zuwa tattara wannan rahoto, babu duriyarsu.

Goje ya kara da cewa, ana ci gaba da aikin bincike domin ceto su, wanda masu ruwa da tsaki na cikin gida da masu kwale-kwale ke gudanarwa, karkashin kulawar hukumar ta SEMA.

Ya ci gaba da cewa, hukumar ta kammala tantance kayan abinci ga daukacin fasinjoji 52, sannan kuma za ta ci gaba da neman wadanda har yanzu ba a san inda suke ba.

Gwamna Mai Mala Buni, ya yi ta’aziyya tare da bayar da gudunmawar naira miliyan 20 da kuma bayar da umarnin yin gyare-gyare ta fuskar harkokin kula da tsaro da rigunan ruwa da kwale-kwale na zamani da kuma horar da matuka jiragen.

Wani bincike da aka aiwatar ya binciko cewa, yawancin abubuwan da suka faru a jihohi kamar Sakkwato, Neja, Kogi da Yobe, na nuni ne da cewa, abubuwa ne da za a iya magance su.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *